✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko Lamido ba ya so za mu saya masa fom din tsayawa takara a PDP – Aminu Jahun

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa, Alhaji Aminu Nuhu ya za su tilasta Gwamna Alhaji Sule Lamido don ya tsaya takarar Shugaban kasa a…

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa, Alhaji Aminu Nuhu ya za su tilasta Gwamna Alhaji Sule Lamido don ya tsaya takarar Shugaban kasa a badi, inda za su yanka masa fom din takara a cikin jam’iyyarsu ta PDP ko da ba ya so.
Alhaji Aminu Jahun ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a ofishinsa  ranar Talata, inda ya ce Shugaba Jonathan bai isa ya hana Gwamna Lamido tsayawa takara ba, kuma ba sa shakkar Gwamna Lamido zai fito takarar Shugaban kasa a zaben 2015.
Ya ce saboda Jonathan har arna an kira su a zaben da ya gabata na 2011, amma duk da halaccin da suka yi wa Jonathan bai hana gwamnatinsa cin mutuncin jama’ar Arewa ba, inda ake fama da talauci da rashin tsaro.
Ya ce ganin kwamacalar gwamnatin Jonathan ne ya sa suka ce dole Lamido ya fito neman kujerar shugabancin kasar nan a 2015, domin a samu gyara a hada kan jama’ar kasar nan da ceto ta daga halin da ta samu kanta a ciki.
Ya ce idan Lamido ya samu nasarar zama Shugaban kasa za a samu canji na alheri cikin lokaci kankane tare da ingantar tattalin arzikin kasa da zaman lafiya.