✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ’yan Najeriya za su ga ci gaba a wa’adin Buhari na biyu?                        

Tun bayan shigarsa harkokin siyasa da takararsa ta farko ta neman shugabanci a shekarar 2003, Shugaban Kasa Muhammadu ke samun tagomashi da goyon baya daga…

Tun bayan shigarsa harkokin siyasa da takararsa ta farko ta neman shugabanci a shekarar 2003, Shugaban Kasa Muhammadu ke samun tagomashi da goyon baya daga miliyoyin ’yan Najeriya da suka yi amana cewa zai iya fitar da kasar nan da ga tarin matsalolin da suka yi mata dabaibayi.

Bayan yunkurinsa na hawa shugabancin kasa sau uku ba tare da nasara ba, zabubbukan da duka ya yi ikirarin cewa an yi masa murdiya, a karshe dai Buhari ya samu nasara a shekarar 2015 a zaben da galibi aka yi amana cewa ’yan Najeriya sun mara wa Buhari da jam’iyarsa ta APC baya ne da zimmar cewa za a samu sabon salo na shugabanci, wanda zai kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi sassan Najeriya, musamman ta Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Shugaba Buhari, za a iya cewa ya yi rawar gani wajen ingantuwar tsaro a  Arewa maso Gabas, duk da cewa ana samun hare-hare a wasu yankunan yankin. Akwai bukatar kara kaimi wajen karfafa wa jami’an tsaro gwiwa, ba a shiyar Arewa maso Gabas kadai ba, har ma da sauran sassan da ke fuskantar matsalar tsaro. A jihohin Katsina da Zamfara da Sakkwato ’yan bindiga na hallaka jama’ar kauyuka wadanda ba su ji ba ba su gani ba kusan duk rana ta Allah.

A daidai lokacin da Shugaban Buhari ya fara wa’adin mulki karo na biyu, kuma na karshe a tsarin mulki, abu ne da ya dace ya yi, shi ne dubi ga irin gagarumin goyon baya da kuma tsammani da ’yan Najeriya ke da shi a kansa na magance musu tarin matsaloli da suke ci musu tuwo a kwarya.

A wa’adin mulki na farko Shugaaba Buhari ya dauki tsawon watannni kafin ya nada ministocinsa, wanda a wancan lokaci aka yi tsammanin cewa ya dauki lokaci ne domin zabo mutane hazikai, to amma da dama sun yi sukar irin mutanen da suka ga an nada a matsayin ministoci. Fata a yanzu shi ne Shugaban Kasa zai yi gaggawar nada ministocinsa domin ci gaba da aiki babu kama hannun yaro. Matsalar cin hanci da rashawa za a iya cewa ita ce kan gaba wajen mayar da kasar nan baya, wacce kuma ake ganin gwamnatin Buhari za ta magance. Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta yi nasarori wajen karbo kudade da kadarorin gwamnati daga hannun jami’an gwamnatocin da suka gabata. To amma a nan, akwai bukatar a wa’adin mulkin na biyu Buhari ya kara kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar tabbatar da cewa babu shafaffu da mai kamar yadda ake zargin cewa ana kawar da kai daga al’mundahana da wadansu jami’an gwamnati mai ci ke yi.

A jawabinsa na bikin Ranar Dimokuradiyya ranar 12 ga Yuni, Shugaban Kasa ya yi alkawrin cewa gwamnati za ta ci gaba da inganta walwalar ’yan Najeriya ta hanyar bunkasa tattalin arziki. Gwamnati ta bullo da tsare-tsare na bunkasa harkar noma, ta hanyar ba da tallafi ga manoma a karkashin wani shiri na Babban Bankin Nageriya (CBN), duk da cewa wannan tsari ya yi nasara a wasu jihohi, akwai bukatar gwamnati a wannan karo ta tabbatar da cewa tallafin ya kai ga manoma na ainihi, musamman a yankunan karkara.

Babban abin tambaya da kuma sanya ido a wannan wa’adin mulki na biyu shi ne ko Shugaban Kasar zai kawo canjin da al’umma ke fata?

Shugaban Kasa a lokuta da dama ya dora alhakin rashin samar da ci gaba da ake bukata kan irin al’mundahana da ya zargi gwamnatocin baya da aikatawa. To shekara hudu na wa’adin farko sun isa a ce ’yan Najeriya sun ga sauyi mai ma’ana a kwanakin farko na wannan wa’adi na biyu.

Wani abu da fadar Shugaban Kasa ke ba da hujja a kai, wanda kuma ta ce ya hana ruwa gudu a wa’adin farko shi ne, rashin kyakkyawar alaka a tsakanin Bangaren Majalisar Dokoki da fadar Shugaban Kasa. Tun farko dai fadar Shugaban Kasa ta nuna adawarta da shugabancin majalisun tarayya a wancan lokaci.

A yanzu da Jam’iyyar APC da fadar Shugaban Kasa suka samu nasarar dora wadanda suke goyon baya a matsayin shugabannin majalisar, ko za a samu sauyi da al’umma ke fata? Lokaci ya yi da Shugaban Kasa Buhari zai tashi tsaye wajen tabbatar da cewa ya yi aiki babu kama hannun yaro don samar da ci gaba mai dorewa. ’Yan Najeriya dai sun mara wa Shugaban Kasa Buhari baya ne a tsarin mulkin dimokuradiya saboda irin rawa da suke ganin ya taka lokacin mulkin soji. ’Yan Najeriya kuma za su ci gaba da bayyana irin nasarori ko akasin haka a karshen shugabancinsa na farar hula.

Umar Ahmad Abubakar

[email protected]