✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko zaben Abe zai kawo sauyi kan rigimar Amurka da Koriya ta Arewa?

A ranar Larabar da ta gabata ne aka sake zaban Shinzo Abe a matsayin Firaministan Japan, lamarin da ya baiwa jam’iyya mai mulki da kawancenta…

A ranar Larabar da ta gabata ne aka sake zaban Shinzo Abe a matsayin Firaministan Japan, lamarin da ya baiwa jam’iyya mai mulki da kawancenta damar samun rijaye a zaben, haka zalika nasarar na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan kafin ziyarar Shugaban Amurka, Donald Trump zuwa kasar, ziyarar da ake ganin za ta fi shafar batun takalar Koriya ta Arewa.

Shugaba Abe dan shekaru 63 ya karbi mulki ne a shekarar 2012 bisa alkawarin samar da ci gaba a fannin tattalin arziki da bunkasa harkokin tsaro. Jam’iyyarsa ta Liberal tare da kawancensu sun samu kashi biyu bisa uku a zaben da aka yi a ranar 22 ga watan Oktoba, abin da zai bawa fira-ministan karfin gwiwa a fafutikarsa ta samar da ci gaba a kasar da samar da sauyi a kundin tsarin mulki. Ana sa ran ya kafa gwamnati da za ta zo da kasafin kudi kafin nan da Watan Maris na 2018, kasafin da zai bada kulawa ta musamman kan yara da bunkasa harkokin masana’antu.