✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Eagles Rohr da NFF sun sa zare

A ranar Litinin da ta wuce ne aka yi musayar yawu a tsakanin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Gernot Rohr da Shugaban Hukumar NFF…

A ranar Litinin da ta wuce ne aka yi musayar yawu a tsakanin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Gernot Rohr da Shugaban Hukumar NFF Amaju Pinnick.

A wata hira da kafar talabijin Channels TB ta yi da Mista Amaju Pinnick a ranar Litinin da ta wuce ya bayyana cewa kafin hukumar ta sabunta wa kocin kwantaragi sai ya amince zai rika gayyatar ’yan kwallon gida al’amarin da Rohr ya nuna hakan ba za ta sabu ba.

A wata hira da aka yi da kocin ya ce Hukumar NFF ba ta da ikon ta tursasa masa wajen gayyatar ’yan kwallon da ke wasa a gida kuma ba zai taba amincewa da wannan doka ba.

Rohr wanda kwantaraginsa zai kare a badi, rahotanni sun ya ce babu wanda ya isa ya tursasa shi wajen zakulo ’yan kwallon da ba su dace ba  walau a gida ko a waje.

Mista Amaju Pinnick  ya ce zai tabbatar an sanya dokar tilasta wa kocin gayyatar ’yan kwallon gida kafin a sabunta masa kwantaragi yayin da kocin ya ce atafau.

Jama’a dai sun zuba ido su ga yadda dambarwar za ta kaya.

Kawo yanzu dan kwallon kulob din Enyimba Ifeanyi Anaemena ne kadai a jerin ’yan kwallo 23 da kocin ya gayyato wadanda suka buga wa Najeriya wasa biyu na neman gurbi a gasar cin Kofin Afirka da za a yi a shekarar 2021.