✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bada umarnin a tsare Bello Adoke tsawan kwana 14

Wata babbar kotu a Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja ta bai wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) umarnin ta tsare…

Wata babbar kotu a Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja ta bai wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) umarnin ta tsare tsohon ministan shari’a Mohammed Bello Adoke na tsawon kwana 14 yayin da ake ci gaba da bincike a hannunta har na tsawon mako biyu.

Mai Shari’a Othman A. Musa, ne ya bayar da umarnin a tsare tsohon ministan shari’ar na tsawon kwana 14 yayin da ake ci gaba da bincike da kuma yi masa shari’a.

A yau Juma’a ne aka bayar da umarnin bayan da hukumar EFCC ta damke Adoke jim kadan bayan saukarsa a filin jirgin sama na Abuja a yammacin jiya Alhamis, inda ‘yan sandan kasa-da-kasa na Interpol suka yi masa rakiya daga Dubai.