✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ce ’yan sanda su cire hannusu daga wata shari’a

Babbar Kotun Jihar Kano a karkashin jagorancin Mai shari’a A. T. Badamasi ta aike wa Mataimakin Sufeton ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta daya…

Babbar Kotun Jihar Kano a karkashin jagorancin Mai shari’a A. T. Badamasi ta aike wa Mataimakin Sufeton ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta daya da ke Kano tare da wadansu ’yan sanda takardar jan kunne a kan su tsame hannunsu daga wata shari’a da ke gaban kotun, ko ta dauki mataki a kansu.
Takardar gargadin, mai lamba K/48/2016 tana bayani ne kan shari’ar da ake yi tsakanin Safiyanu danfulani da Sulaiman Usman da wasu mutane.
Sauran ’yan sandan da kotun ta yi wa gargadin sun hada da ASP Alpha Jibrin da DSP Kalad Shaman da O.C Yakubu Isyaku da Saje Tahir.
Tunda farko lauya Bashir Sabi’u ne ya garzaya gaban kotun inda yake kalubalantar jami’an ’yan sandan saboda yaga takardar umarnin kotu da suka yi tare da tsare shi da suka yi.
Barista Bashir Sabi’u ya yi wa Aminiya karin haske cewa “Bayan an kai musu umarnin kotu sai suka yayyaga ta tare da zagin alkalin. Lokacin da na je in yi musu bayani a kan su girmama umarnin kotu
a nan suka kama ni suka tilasta ni yin wani rubutu. Ba su sake ni ba sai da aka ba su Naira dubu 100.”
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Rundunar ’Yan sandan na Shiyya ta daya ya ci tura kasancewa Kakakinta ASP Rabilu Ringim ba ya daukar waya kuma bai amsa sakon tes da aka yi masa ba.