Search
Subscribe
Kotu ta dage shari’ar tsohon Sarki Sanusi II

Malam Muhammadu Sanusi II

Kotu ta dage shari’ar tsohon Sarki Sanusi II

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage sauraren karar da tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya shigar inda yake neman kotun ta hana Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin-Hanci da Rashawa ta Jihar Kano yin bincike a kansa.

Wadanda ake karar sun hada da hukumar da shugabanta Barista Muhyi Magaji Rimin Gado da Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar.

Idan za a iya tunawa Aminiya ta ruwaito cewa tun ranar 6 ga Maris  kotun ta bayar da umarnin  kowa ya tsaya a matsayinsa har sai ta saurari karar da tsohon Sarkin ya shigar gabanta.

Yayin da aka fara sauraren karar a kotun, lauyan wanda ake kara na farko da na biyu Barista Usman Fari ya rubuta wata takarda da ta ci karo da abin da ake kara a kai.

Haka shi ma lauyan wanda ake kara na uku da na hudu Barista Khalifa Hashim ya rubuta takarda da yake kalubalantar hurumin kotun game da sauraron wannan kara.

Da yake mayar da jawabi Lauyan mai kara Nasiru Dangiri (SAN) ya nemi kotun ta kara musu lokaci don yin nazari tare da mayar da martani game da kudirin da wadanda ake kara suka yi cewa kotun ba ta da hurumin saurarar wannan kara.

Sai dai alkalin kotun Mai shari’a Lewis Allagoa ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Maris.

Hukumar dai ta fara bincike kan tsohon Sarkin ne da Makaman Kano Alhaji Sarki Ibrahim da Sarkin Shanun Kano Alhaji Shehu Dankadai a kan wasu filaye da ke Gandun Sarki a Hotoron Arewa da kuma Bubbugaje.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin