Kotu ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai

A yau Alhamis Kotun Daukaka Kara da ke jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar zaben Nasiru El-Rufa’i a matsayin zababben Gwamnan jihar Kaduna.

Dan takarar Gwamnan Kaduna na jam’iyyar PDP Alhaji Isa Mohammad Ashiru, ne ya shigar da shigar da karar kotun don kalubalantar nasarar zaben Gwamna El-Rufa’i. Kotun ta ce dan takarar PDP baida cikakken hujjar da kotun zata gamsu da ita.

Manyan Alkalai biyar ne suka jagoranci shari’ar wadanda suka hada da: UI Anyanwu, HAO Abiru, TY Hassan, BM Ugo da BB Aliyu.

Cikakken rahoton na nan tafe.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya