✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar wa Gwamna El-Rufa’i kujerarsa

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta Kaduna ta tabbatar wa Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i kujerarsa a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna da aka yi a…

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta Kaduna ta tabbatar wa Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i kujerarsa a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna da aka yi a watan Maris, 2019.

Alkalin Kotun Ibrahim Bako wanda ya yanke hukuncin hakan a ranar Litinin da ta gabata ya yi watsi da karar da dan takarar  Jam’iyyar PDP, Isa Ashiru ya shigar saboda rashin kwararan shaidu.

Da yake bayani ga manema labarai a harabar kotun a Kaduna, Lauyan Gwamna El-Rufa’i Abdulhakeem Mustapha (SAN) ya ce kotun ta gamsu cewa mai karar ba ya da shaidun da za su nuna cewa Nasir El-Rufa’i bai ci zabe ba.

Ya ce kotu ta gamsu cewa masu karar sun bata mata lokaci ne saboda rashin shaidu wanda hakan ya sa aka yi watsi da karar tare da bayyana Gwamna Nasir El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben.

Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar  Mista Felid Hassan Hyet ya bayyana rashin jin dadinsu kan hukuncin kotun inda ya ce jam’iyyarsu za ta fitar da matsayinta a kan hukuncin nan ba da dadewa bayan sun tattauna da lauyoyinta da kuma dan takaransu.

Ya nemi magoya bayansu  su kara hakuri su kuma saurari matsayin jam’iyyar tasu nan ba da dadewa ba.