✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matar da ke auren maza biyu a kurkuku

Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta bayar da umarnin tsare matar nan da ake zargi da auren maza biyu…

Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano ta bayar da umarnin tsare matar nan da ake zargi da auren maza biyu tare da mijinta na biyu da wata mata da ta yi mata walicci bisa tuhumarsu da laifin yin aure a kan aure.

A zaman kotun da aka yi a ranar Talatar da ta gabata kotun ta gano cewa matar mai suna Hauwa Aliyu sun yi aure da mijinta na biyu Bala Abdussalam ne ba tare da daurin aure yadda Musulunci ya tsara ba, domin matar da kanta ta shaida wa kotu cewa auren nasu an daura shi ba tare da limami ba saboda an yi shi ne a sirrance. Kuma ta shaida wa kotun cewa wata ’yar uwarta mace ce ta yi mata walicci.

Har ila yau a bangaren mijin  na biyu ya shaida wa kotun cewa shi ya yi wa kansa walicci lamarin da kotun ta ce ba ta da ja a kai saboda shari’a ta ba namiji damar tsayawa kansa walicci. Sai dai kotun ta ki karbar hanzarinsa na rashin masaniya kan cewa mijin matar na farko bai sake ta ba.

Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya bayar da umarnin tsare matar da mijinta na biyu da matar da ta yi mata walicci a kurkuku inda kuma ya dage ci gaba da sauraren shariar zuwa ranar 21 ga watan Afrilu.