✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tura wata gidan yari kan kona uwa da danta dan wata 10

Kotun Majistare ta Daya da ke  Chediya GRA, Zariya ta tasa keyar wata mata mai suna Nnennaya Edmond zuwa gidan yari zuwa ranar 15 ga…

Kotun Majistare ta Daya da ke  Chediya GRA, Zariya ta tasa keyar wata mata mai suna Nnennaya Edmond zuwa gidan yari zuwa ranar 15 ga watan Oktoba inda za a ci gaba da sauraron karar da ake zarginta da kona wata mata da danta dan wata 10 da haihuwa da ruwan zafi.

Da yake gabatar da wadda ake tuhumar a gaban kotun, Sufeton ’Yan sanda Mannir Nasir ya ce a ranar Talata 10 ga watan Satumba wata mata mai suna Mary Ejoemah ta kai rahoto ofishinsu na yanki da ke Danmagaji cewa Nnennaya Edmond ta kona ’yarta mai suna Gloria Cyril da danta da ruwan zafi.

Da dan sanda mai gabatar da kara ya kammala karanta tuhumar da ake wa Nnennaya Edmond sai kotu ta tambaye ta ko ta aikata laifin da ake tuhumarta, inda ta ce ba ta aikata ba. =Wanda hakan ya sa Mai shari’a Abubakar Aliyu Lamido ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan yarin kafin ci gaba da sauraron shari’ar.

A halin da ake ciki Gloria Cyril da danta suna kwance a asibitin St. Luke’s da ke Wusasa inda suke jinya.

Bayyan kammala sauraran karar, Aminiya ta ji ta bakin mijin matar da aka kona da danta, inda ya ce, “Muna zaune ne a gida daya kuma kowa da barayinsa, kuma ko wajen dafa abinci ba mu hada ba. Kuma ruwan da ta watsa musu, matata ta dora kuma a sashinta domin kowa wurinsa daban ne. Yanzu muna jira ne mu ji abin da kotu za ta yi duk da ta ki amincewa da laifinta, Kuma idan ka duba hannunta ai da kuna wanda ya isa ya zama shaida.”