✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa matashin da ya daddatse matar aure hukuncin kisa a Jigawa

Babbar Kotu ta Hudu da ke Dutse fadar Jigawa ta yanke wa wani matashi mai suna Rilwanu Malam Hassan mai shekara 25 hukuncin kisa ta…

Babbar Kotu ta Hudu da ke Dutse fadar Jigawa ta yanke wa wani matashi mai suna Rilwanu Malam Hassan mai shekara 25 hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan da ta same shi da laifin daddatse wata matar aure da adda a gidanta a shekarar 2013.

Da yake yanke hukuncin alkalin kotun Mai shari’a Ubale Taura ya ce an samu matashin da laifin kisan kai bisa dogaro da kwararan shaidu da kotun ta gamsu da su cewa shi ya aikata laifin, don haka kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar ratayewa kamar yadda yake kunshe a karkashin sashi na 221 (b) na kundin manyan laifuffuka na jihar. Rilwanu mutumin kauyen Samamiya ne da ke karamar Hukumar Birnin Kudu ya daddatse matar mai suna Suwaiba Sagir mai shekara 40 a kauyen Samamiya.
Shaidu sun tabbatar wa kotun cewa lokacin da Rilwanu ya aikata laifin sai ya gudu ya fada cikin wata tsohuwar rijiya ya boye aka yi ta nemansa ba a same shi ba sai daga baya ne ’yan sanda suka gano shi a cikin tsohuwar rijiya suka kama shi suka gabatar da shi a gaban kotu.
dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun Kofur Muhammed Muhammed ya gabatar mata da shaidunsa shi kuma wanda ake tuhuma ya gaza kare kansa, lamarin da ya sa kotun ta yanke masa hukunci duk da cewa ’yan uwansa sun yi ikirarin yana da tabin hankali, kuma shi kansa ya ce ya dauki matakin ne a lokacin yana cikin wani hali na tabin hankali.
Mai shari’a Ubale Ahmed Yaura ya ba wanda aka yanke wa hukuncin wa’adin wata uku don ya daukaka kara in bai yarda da hukunci ba.