✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yarda a kashe aure saboda rashin bandaki

Wata kotun Indiya ta bai wa wata mata izinin sakin mijinta saboda rashin bandaki a gidansu, har ta kai ga sai  ta fita waje sannan…

Wata kotun Indiya ta bai wa wata mata izinin sakin mijinta saboda rashin bandaki a gidansu, har ta kai ga sai  ta fita waje sannan ta kewaya.

Kotun mai warware rikicin iyalai da ke Arewa maso yammacin Jihar Rajastan ta yanke hukuncin ne ranar 18 ga Agusta, in da matar ta samu nasarar karar da ta gabatar cewa ya kasa gina bandaki a gidansu tsawon shekara biyar da aurensu.

Mai shari’a rajendra Kumar Sharma  ya ce mata a kauyukan na fama da wahalar jira har dare ya yi duhu, sannan su samu yin bahaya a wajen gidajensu.

Alkalin ya yi nuni da cewa kashi a waje na tattare da barazanar baza cututtuka a Indiya, al’amarin da ya ce abin kunya ne kuma cutarwa ga mata, kuma aka tauye musu hakkin samun kyakkyawan muhalli a cewar lauya mai Karen hakkin mata Rajesh Sharma a hirarta da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Ana bayar da izinin sakin aure ne kawai a Indiya in an samu hujjar da ta nunba  keta haddi da azaftarwa da bijiro da yawan bukatar kudi a gaban kotu.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da aure ya rabu saboda matsalar rashin makewayi ba.

Bara ma wata mata ta ki yarda a daura mata aure a Jihar Utttar Pradesh bayan da mai neman aurenta ya ki gina bandaki a gidan da ma’auratan za su zauna.

Kuma a Yunin da ya gabata wata mata ta ki komawa gidan surukanta har sai sun gina bandaki.

Firayiminista Narendra Modi ya yi alkawari gidana makewayi a kowane gida nan da shekarar 2019 don shawo kan bahaya a fili. Kuma gwamnati ta ce a halin yanzu an gidan bandaki har miliyan 20 tun da aka bullo da shirin cikin shekarar 2014.