Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Kotun koli ta soke zaben Gwamnan Bayelsa

Lyon-Diri-da Biobarakuma Degi-Eremieoyo

Kotun koli ta soke zaben Gwamnan Bayelsa

Kotun kolin Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa David Lyon da mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremieoyo.

Kotun ta soke zaben David Lyon, na jam’iyyar APC wanda ya rage kwana guda a rantsar  da shi a matsayin Gwamnan jihar.

Alkalan kotun wanda ya kunshi mambobi biyar, Mai shari’a Mary Odili ce ta jagoranci yanke hukuncin yau Alhamis, sun ce sun soke zaben David Lyon, ne saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa hukumar zaben kasar takardun bogi domin a barsa ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.

An samu bayanan bogin ne a takardar CF 001 na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, wanda Degi-Eremieoyo ya mika ga Hukumar INEC saboda kawai takarar zaben 16 ga watan Nuwambar 2019.