Da Dumi Dumi

Kotun Shari’ar Musulunci ta Kazaure ta bukaci dan Majalisar Tarayya ya bayyana a gabanta

Babbar Kotun Shari’ar Musulinci (Upper Shari’a Court) da ke Kazaure a Jihar Jigawa ta umarci dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kazaure da Roni da Giwa da’Yankwashi Alhaji Bashir Adamu ya bayyana a gabanta a ranar 13/1/2014 tare da lauyansa.
Alkalin Kotun Mai shari’a Alhaji Jazuli Rabi’u ya bayyana haka lokacin da yake amsar karar da wani Alhaji Muhammed Sadis Abdullahi Kazaure ya shigar akan dan majalisar a gaban kotun a ranar Litinin da ta gabata, inda yake kukan dan majalisar ya sa an rubuta masa takardar cin mutunci.
Alkalin ya umarci lauyan dan majalisar ya gabatar da adireshinsa da sunan kamfanin lauyoyinsa da kuma cikakken sunansa a gaban kotun kuma shi ma ya bayyana a gaban kotun a ranar da aka ambata.
Ya nuna damuwarsa saboda rashin halartar wanda ake karar da lauyansa a zaman da ya gabata, inda ya ce bayanin ta waya kan rashin zuwansu ba madogara ba ce a wurin kotun. Sai ya umarci magatakardar kotun wanda ya ce lauyan wanda ake karar ya sanar da shi cewa suna da wata shari’a a Abuja da zai kare, shi ne ya sa bai samu halartar zaman kotun ba, inda ya ce magatakardar ya sake sanar da su sabuwar ranar da kotun za ta sake zama domin su halarci zaman kotun a karo na biyu, ya ce idan suka ki halartar zaman kotun ba za ta amince da wani bayani ba domin ya zama tamkar raini ne ga kotun.

Share