✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun sojoji ta kori soja daga aiki kan yi wa ’yar gudun hijira fyade

Kotun Musanmman na Hukunta Sojoji ta Runduna ta 7, ta yanke wa wani soja hukuncin kora daga aiki saboda yi wa wata yarinya ’yar gudun…

Kotun Musanmman na Hukunta Sojoji ta Runduna ta 7, ta yanke wa wani soja hukuncin kora daga aiki saboda yi wa wata yarinya ’yar gudun hijira mai shekara 14 fyade a Maiduguri.

Da yake yanke hukunci bayan sauraron karar tare da karbar rahoton Kwamitin Bincike, Babban Alkalin Kotun Manjo Janar Yakubu Auta, ya ce, “Yanke irin wannan hukunci a kan wannan soja Laftanan Sojin Sama Martins Ewerem ya zama wajibi saboda  yadda ya ci zarafin wata yarinya mai suna Zara Ali, wadda ba ta wuce shekara 14 ba da take sansanin gudun hijira na Bakassi da ke garin Maiduguri. Wannan yarinya daga an aikensu debo ruwa ne sojan saman ya ganta ya kama ta tare da  shiga da ita cikin daji ya yi mata fyade tare da hana ta kuka al’amarin da ya sanya daga baya dole sai da aka kai ta asibiti don duba lafiyarta. Kuma bayan an kai kararsa wajen kwamandansa a wurin aiki sai ya yi masa rashin kunya.”

Alkalin ya ce, “Duk da cewa sojan ya amsa zargin da ake yi masa na cin zarafin yarinyar tare da yi mata fyade kuma bai wahalar da kotu ba, amma dole ne kotu ta yanke masa hukunci don ya zama darasi ga na baya. Shi ya sa kotun ta yi nazari tare da yanke masa hukuncin kora daga aiki a kan laifi na farko da rage masa mukami a laifi na biyu da kuma daure shi na tsawon shekara 3.”

Ya ce wannan zai iya gyara halayen wadansu sojoji da suke da nufin yin irin haka a gaba.

Alkalin ya ce, “Wajibi ne mutane su fahimci cewa mu sojoji muna kokarin kare hakkin dan Adam, don haka ba za mu yarda irin wannan ya sake aukuwa a tsakanin sojoji ba, domin za a hukunta duk wanda ya aikata irin wannan kamar yadda doka ta tanada.’’