✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku yafe mana za mu dauki matakai masu tsauri a Kaduna – El-Rufai

A jawabin rantsar da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a karo na biyu, ya roki jama’ar jihar Kaduna da su yafe masa akan daukan tsauraran…

A jawabin rantsar da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a karo na biyu, ya roki jama’ar jihar Kaduna da su yafe masa akan daukan tsauraran matakan da za a yi wajen bunkasa jihar.

Gwamnan ya ce, za a baiwa mata ma’aikatan gwamnati wadanda suka haihu hutun wata shida, don tabbatar da lafiyar jaririn da suka haifa da samun kyakkyawan shayarwa.

El-Rufai ya kara da cewa, wannan gwamnati za ta maida hankali ne akan bukatun ’yan jihar kuma wannan gwamnatin ta kowa ne dan jihar ne.