✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kula da tarbiyyar yara (2)

Idan kuna biye da mu, satin da ya gabata mun kawo muku bayani a kan kula da tarbiyyar yara. Za mu ci gaba in Allah…

Idan kuna biye da mu, satin da ya gabata mun kawo muku bayani a kan kula da tarbiyyar yara. Za mu ci gaba in Allah ya yarda.

Afuwa da nuna tausayi

Wannan ba ya nufin a saki yaro kara zube har ya sangarce.Manufa  duk lokacin da yaro ya yi laifi kuma aka nusar da shi ya fahimci kuskurensa, to sai a yafe masa kada a ce kuma sai an hore shi. Domin yin haka zai sa shi ma ya koyi rangwame da yin afuwa ga mutane. Kuma a rika tausaya  masa kada a dora masa aikin da ya fi karfinsa. Haka nan a koya masa tausayin kannensa. Hatta dabbobi kada a bari yaro ya saba da cin zalinsu. Maimakon haka a nuna masa yadda zai ba su abinci ya kula da su. Koya wa yaro tausayi ba ya nufin a bari yaro ya zama rago, matsoraci, Hausawa suna cewa, “Matsoraci ba ya zama gwani.” Don haka a yi hattara.

Kula da aikin gida

Aiyukan gida suna da yawa,don haka sai a dubi wanda ba zai cutar da yaro ba a saka shi ya rika yi lokaci-lokaci har ya koya. Koda akwai ’yar aikin gida, yana da kyau yaran gida su rika taimakawa. Domin kuwa idan yau mu ne, ai gobe ba mu ne ba. Musamman girki lallai a koya wa yara. Ta hanyar aikin gida yaro yakan koyi tsabta kamar wankin kaya da kwanuka da shara da sauran abubuwa masu muhimmanci. Kuma ita ma ’yar aikin za ta sami sauki ta ji dadin yin aikin sosai.

Kada yaro ya zama mai rowa da kwadayi

Yawanci mutum mai rowa ya cika kwadayi domin kuwa, “Wanzami ba ya son jarfa.” Yana da kyau iyaye su sa ido su tabbatar yaro bai zama marowaci ba. Za a iya gane haka ta yadda yake mu’amala da sauran yara. Kuma da zarar an fuskanci haka, sai a yi kokari a tsawatar masa domin kada ya tashi da wannan mummunar dabi’a. Kuma kada a sake ya zama mai kwadayi, “Kwadayi mabudin wahala.” A nuna masa kyauta amma ban da almubazzaranci. Kada ya zama  mai wulakanta  duk abin da ya zo hannunsa. Yana da kyau yaro ya san tattali, wato “A ci, a sha, a rage don gobe.”

 Kula da tsafta

A koya wa yaro yadda zai kula da jiikinsa da sauran abubuwa. Misali a koya masayin  wanka  a kalla sau biyu a rana.Haka nan wankin baki sau biyu. Kuma duk lokacin da zai ci abinci da bayan ya ci ya wanke hannayensa ya kuskure bakinsa. A nuna masa sanya kaya masu tsabta da lura da su kada nan da nan ya bata su kamar an tono shi daga rami. Haka nan a nuna masa yadda zai ninke kayansa kada ya rika zubar da su kaca-kaca a ko’ina. Kuma idan yaro ya yi wasa ya gama, a nuna masa yadda zai kwashe kayan wasan nan tsaf, ya je ya ajjiye su wuri daya.

Kada a sake yaro ya cika wasa da yawa

Yara suna da son wasa musamman wannan zamani da ya kawo mana abubuwan dauke hankali, wanda ko babba ma sai ya yi a hankali idan ba haka ba kuwa  mutum zai ta bata lokacinsa bai lura ba. Don haka kada a bari yaro ya saba da kallon talabijin tun daga dawowa daga makaranta har tsakar dare. Sai dai, “Idan bera da sata, daddawa na da wari.” Domin kuwa wasu iyayen su ne  gwanayen kallon fina-finai, a irin wannan yanayi  ba za ka iya hana yaro kallo ba. Saboda haka iyaye su rage kallon fina-finan shirme. Wani lokaci kuma akan bar yaro ya yi ta yin ‘games’ a waya ba kwaba ba kyara. Wannan yakan hana shi karatu da yin wasu muhimman abubuwa a gida.Sannan kuma wannan ‘game’ yakan haddasa rigima a tsakanin yara. Ba za a hana yara wasa ba kwata-kwata, amma “Taba kidi taba karatu.” Kuma ba kowane irin kayan wasa za a sayo wa yaro ba. Haka nan kuma kada a bar yara su kadai suna wasa na tsawon lokaci ba tare da an san irin wasan da suke yi ba.

Za mu ci gaba!