✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kulob din Manchester United ya fara zawarcin Thiago Alcantara

Kulob din Manchester United ya fara shirin dauke dan wasan tsakiya a kulob din FC Barcelona da ke Sifen Thiago Alcantara muddin bai samu nasara…

Kulob din Manchester United ya fara shirin dauke dan wasan tsakiya a kulob din FC Barcelona da ke Sifen Thiago Alcantara muddin bai samu nasara a kan saye Cesc Fabgrebas daga kulob din ba.
Shi dai sabon Kocin Manchester United Dabid Moyes ya dade yana zawarcin Acantara a lokacin da yake horarwa a kulob din Eberton da ke Ingila amma saboda rashin kudi ta sanya kulob ya kasa cinikin dan kwallon a wancan lokaci don haka a wannan karo da ya koma Manchester United sai ya sake tayar da batun.
Fabregas, wanda aka dade ana rade-radin zai koma Manchester United a shekaranjiya Laraba ya bayyana cewa “a iya saninsa har zuwa wannan lokaci babu wanda ya tuntube shi a kan maganar canza sheka, hasalima dai ya dade yana mafarkin buga kwallo a FC Barcelona don haka ba ya tunanin barin kulob din a halin yanzu”.
Wadannan kalamai ne suka jefa kulob din United cikin shakku ko dan wasan zai iya canza sheka zuwa wajensu don haka suke tunanin karkata akalarsu zuwa Thiago Alcantara da ya nuna sha’awar barin FC Barcelona kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Rahotanni sun nuna kulob din Barcelona zai iya sayar da Thiago Alcantara a kan Fam miliyan 15 don haka akwai yiwuwar dan kwallon ya koma United kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Kulob din United ya fara tunanin yin garambawul ne ga ’yan wasan tsakiyarsa da mafi yawansu sun tsufa kafin a fara kakar wasa mai zuwa.