✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kulob din Sardauna ya lashe kofin Dasuki na ’yan kasa da shekara 25

Bayan fafatawar kwallon kafa ta wata daya, kungiyar kwallon kafa ta  Sardauna ce ta lashe kofin Honorabul  Abdussamad Dasuki, dan majalisar dokokin Jihar Sakkwato, mai…

Shugaban karamar Hukumar Tambuwal, Hon. Sambo Modo ne yake mika kofin lashe gasar ga kaftin din Sardauna united.Bayan fafatawar kwallon kafa ta wata daya, kungiyar kwallon kafa ta  Sardauna ce ta lashe kofin Honorabul  Abdussamad Dasuki, dan majalisar dokokin Jihar Sakkwato, mai wakiltar mazabar Tambuwal ta Gabas.
Kulub din Sardauna ya samu nasarar lashe kofin ne bayan ya jefa kwallo daya a ragar ta Talba a wasam karshen da suka fafata a karshen makon jiya.
Kimanin kungiyoyin kwallon kafa takwas ne suka fafata a gasar.  Kulob din Sarkin Shanu ne ya zo na uku.
A jawabinsa jim kadan da kammala wasan, wanda ya dauki nauyin gasar Honorabul Dasuki wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da aikin gona a majalisar dokokin Jihar Sakkwato ya ce ya sanya kofin ne don karfafa hadin kai da fahimtar juna a tsakanin matasa. Alhaji Malami danbafashi ne ya wakilci Honorabul Dasuki.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban karamar Hukumar Tambuwal Honorabul Sambo Bello ya jinjinawa Honorabul Dasuki a kan sanya kofi a tsakanin matasa.  Ya ce ko shakka babu yin haka zai karfafa hadin kan matasa a Jihar kuma hakan zai rage zaman kashe wando da wasu matasa ke yi da hakan ke sa suke shiga cikin ayyukan assha.
Ya sha alwashin cigaba da shirya gasa irin wannan don fafatawa a tsakanin matasa.
kungiyoyi takwas da suka fafata a gasar sun hada da kulob din Sardauna da Talba da Sarkin Shanu da Barade da Mayana da Maina da Jarma da kuma na Turawa.