✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta karrama Shugaban Karamar Karamar Hukumar Kaura

Kungiyar Marubuta ta Majalisar Wakilai da ke Abuja (LWF) ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Kaura da ke Jihar Kaduna da lambar yabo na wanda ya…

Kungiyar Marubuta ta Majalisar Wakilai da ke Abuja (LWF) ta karrama Shugaban Karamar Hukumar Kaura da ke Jihar Kaduna da lambar yabo na wanda ya fi dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar ta fannin ayyukan raya karkara.

Yayin da yake mika lambar yabon a madadin kungiyar da aka gudanar a ofishin Shugaban Karamar Hukumar da ke garin Kaura, Sakataren Shirye-Shirye na Kungiyar, Mista Ogwaje Abraham Jomoh, ya ce sun gano haka ne ta hanyar tantancewar da suka yi sakamakon rangadin da suka gudanar a dukkan kananan hukumomin jihar 23.

Bayan jinjina wa Shugaban Karamar Hukumar kan yadda ya fifita bukatun al’umma a dunkule maimakon na daidaikunsu,  sun bukaci Shugaban ya dore da wannan kyakkyawar manufa da aikin da ya faro.

Da yake mayar da jawabi, Shugaba Karamar Hukumar Dokta Bege Katuka ya gode wa kungiyar da suka zakulo shi daga cikin abokan aikinsa tare da karrama shi kan gudanar da ayyukan da suka rataya a kansa, inda ya dora nasarar hakan ga irin goyon bayan da kananan hukumomin jihar ke samu daga Gwamnan Jihar Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i.

A karshe ya tabbatar wa kungiyar marubutan cewa zai ci gaba tafiya da kowa da kowa wajen aikace-aikacensa tare da gudanar da aiki babu nuna son kai.