✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Afenifere ta gana da Obasanjo kan zaben badi

Mambobin kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere sun yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta Jihar Ogun a ranar Talatar da…

Mambobin kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere sun yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta Jihar Ogun a ranar Talatar da ta gabata, ganawar sirrin da ta kai tsawon sa’a biyu.

Daya daga cikin shugabanin kungiyar, Mista Yinka Odumakin wanda ya zanta da ’yan jarida a madadin kungiyar jim kadan da kammala taron ya ce mambobin kungiyar su jeAbeokuta ne domin rama wa kura aniyarta, domin shi ma ya kai irin wannan ziyara gidan shugaban kungiyar Ayo Adebanjo a Legas.

Ya ce tattaunawarsu da tsohon Shugaban Kasar ta ta’allaka ne kan babban zaben badi, inda suka tattauna alkiblar da al’ummar Yarabawa ya kamata su fuskanta a zaben. “Zaben 2019 abu ne mai muhinmmancin gaske, kana abin sha’awa ne bisa la’akari da manyan ’yan takarar Shugaban Kasa. Lokaci ya yi da ’yan Nijeriya za su yi aiki tare, domin magance matsalolin da kasar nan ke ciki,” inji shi.

Ya ce babban abin da kungiyar Afenifere za ta yi la’akari da shi, shi ne dan takarar da ya yi alkawarin yi wa tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima, abin da wadansu ’yan Kudu ke hankoron ganin ya tabbata don sake fasalin kasar nan.

Ya ce, duk dan takarar da ya yi musu alkawarin yin hakan shi za su zaba. “Nan gaba kadan za mu sanar da dan takarar da za mu mara wa baya a zaben 2019, bayan mun yanke shawarar wanda ya kamata mu mara masa,” inji shi.

A baya dai da yawa daga cikin masu neman takarar Shugaban Kasar nan sun yi ta zuwa wurin Obasanjo domin neman yardarsa, kazalika sun kai wa shugabannin kungiyar Afenifere irin wannan ziyara amma Atiku Abubakar wanda shi ne dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP bai ziyarci Cif Obasanjo ba, sakamakon tankiyar da ke tsakaninsu. Sai dai kuma ya ziyarci shugabannin kungiyar Afenifere a Legas. Haka kuma shi ne dan takarar da a baya-bayan nan ya yi wa al’ummar Yarabawa alkawarin cika musu muradunsu na yi wa tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima don sake fasalin kasa.