✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Dalibai Musulmi ta koka kan rashin tallafin gwamnati a Jigawa

Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN) reshen Jihar Jigawa ta koka kan matsalolin karancin abin hawa da ya damu kungiyar kuma ke kawo cikas a…

Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN) reshen Jihar Jigawa ta koka kan matsalolin karancin abin hawa da ya damu kungiyar kuma ke kawo cikas a ayyukanta na zagaya makarantu don fadakar da dalibai kan ilimin addini.

Shugaban Kungiyar MSS ta Jihar Jigawa, Malam Muhammad Sanka Abdullahi Ahmad ya ce baya ga matsalar abin hawa da ke ci wa kungiyar tuwo a kwarya, gwamnatin jihar ta Jigawa ba ta taimaka wa kungiyar wajen daukar nauyin taronsu a duk shekara.

Ya ce maimakon haka ma wadansu malamai ne da masu hannu da shuni suke daukar nauyin duk wani taro da kungiyar take shiryawa ta fuskar dawainiya da abinci da kuma samar wa jama’a wurin kwana.

Dan haka ya bukaci gwamnatin jihar ta shigo ta taimaka wajen kara wa kungiyar karfin gwiwa kamar yadda take agaza wa wasu kungiyoyi a jihar lura da irin gudunmawar da take bayarwa wajen gyaran tarbiyyar matasa.

Ya ce, sun shirya taron ne da nufin fadakar da matasa, saboda sun fahimci cewa matasa da dama suna bukatar wa’azi domin akwai alamar suna cikin wani yanayi da suke fuskantar matsalolin rayuwa.

Shugaban ya ce saboda haka ne suka hada gwiwa da wata cibiyar horar da matasan sana’o’in hannu domin a koyar damatasan su zamo masu dogaro da kansu. Ya ce a yayin zaman ana gwada wa dalibai maza da mata yadda ake yin man shafawa da hoda da sabulun wanka da na wanki, yayin da wadansu kuma aka kya musu gyaran waya da dinki da saka da sauransu.

Ya ce kungiyar ta dauko daliban ne daga shiyyoyi 12 na jihar da suka hada da Hadeja da Kiri-Kasamma da Kafin Hausa da Malam-Madori da Gwaram da Birnin Kudu da Jahun da Babura da Gumel da Kazaure da kuma Dutse, kuma sun hada da daliban firamare zuwa jami’a.