✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar direbobin Jihar Kebbi ta sami sababbin shugabanni

kungiyar direbobi ta kasa (NURTW), reshen Jihar Kebbi ta kaddamar da sababbin shugabanninta, a taron da aka gudanar a babban dakin taro na masaukin shugaban…

kungiyar direbobi ta kasa (NURTW), reshen Jihar Kebbi ta kaddamar da sababbin shugabanninta, a taron da aka gudanar a babban dakin taro na masaukin shugaban kasa da ke Birnin Kebbi .
Sababbin shugabannnin sun hada da Alhaji Abubakar Garba Kindi Koko a matsayin shugaba da Alhaji Muhammad Shifkau a matsayin mataimakin shugaba na daya da kuma Alhaji Abubakar Aliyu Bakudiga Zuru, ma’aji. Sai Alhaji Aliyu Usman Naira, sakataren kudi. Wadanda aka kaddamar dai su goma sha takwas ne.
A jawabinsa, sabon shugaban ya yi alkawarin za su kwatanta adalci wajen gudanar da nauyin da aka dora musu. Saboda haka ya jawo hankalin ’yan kungiyar su kasance masu gaskiya da mutunta jama’a.
Shi kuma uban kungiya, Alhaji Sani Zauro, Zannan Gwandu jan hankalin ’yan kungiyar ya yi su kasance masu tona asirin miyagun mutane, domin su ke jin maganganan jam’a iri daban-daban idan sun shiga motarsu. Sannan ya nusar da jami’an tsaro su bi kyakkyawan tsari na kare martabar wadanda ke kawo masu rahoton miyagun mutane bata-gari.