✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar kwallon kafa ta Ikulu ta lashe kofin ‘yar takarar majalisa

Kungiyar kwallon kafa ta Ikulu da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna ta doke takwararta ta Jankasa da ci 1-0 a wasan karshe…

Kungiyar kwallon kafa ta Ikulu da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna ta doke takwararta ta Jankasa da ci 1-0 a wasan karshe na kofin ’yar takarar Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC don wakiltar mazabar Zangon Kataf, Misis Maureen Yayock Lekwot da aka buga a filin wasan kwallon kafa na garin Samarun Kataf.

Yayin da take bayani lokacin mika kyauta ga kungiyar da ta yi nasarar, Maureen Lekwot ta bukaci ’yan siyasa su janyo matasa a jiki tare da samar musu da abin yi don nema musu mafita.

Lekwot, ta ce ta shirya wasan ne don hada kan matasan  mazabarta domin fadakar da su yadda za su nisanci sanya kabilanci da addini a harkokin siyasar bana.

Yayin da ta ke mika kyautar, ta taya kungiyar kwallon kafa ta Ikulu murna, tare da yin kiran kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su kan hanyar da ba ta dace ba a karshe su watsar da su bayan sun ci moriyarsu.

“Matasa sun cancanci a ba su dama kuma a sanya su cikin masu ruwa-da-tsaki wajen gina kasa.” inji ta.

Kungiyar Kwallon Kafa ta garin Zangon Kataf ce ta zo ta uku a gasar.