Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kungiyar malaman jami’oin Najeriya ta dakatar da yajin aiki

Kungiyar malaman jami’oin Najeriya ta dakatar da yajin aikin watanni uku da ta shafe ta na yi.

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan cimma yarjejeniya da ta ce ta yi da gwamnatin tarayya a yammacin jiya Alhamis kan bukatunta.

ADVERTISEMENT

Shugaban kungiyar ASUU Farfessa Biodun Ogunyemi ne ya bayyanawa manema labarai hakan, kuma ya ce kungiyar ta gabatarwa gwamnatin tarayya bukatunsu da gwamnati ta rattabawa hannu tun a shekarar 2013.

Kungiyar ASUU ta bukaci jami’o’in kasar da yau Juma’a 8 ga Fabirairu 2019 su dawo bakin aikinsu don ci gaba da gudanar da harkokin jami’o’in.

ADVERTISEMENT