Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Jihar Kaduna ta noma shinkafa sama da buhu dubu 11

Kungiyar Manoman Shinkafa ta  Kasa (RIFAN)reshen Jihar Kaduna, ta samar da shinkafa sama da buhu dubu 11 daga hannun mambobinta a daminar bara.

Shugaban Kungiyar RIFAN  ta Jihar Kaduna Alhaji Muhammad Umar Numbu, ya sanar da haka a yayin zantawar da wakilin Aminiya a garin Zariya a makon jiya.

ADVERTISEMENT

Shugaban  wanda kuma shi ne Dangaladiman Numbu a Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, ya ce shinkafar wadda mambobin kungiyar suka noma a daminar bara ne a karkashin shirin noman shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta samar domin tallafa wa manoman.

Shugaban ya ce nan da shekara mai zuwa kungiyarsa, za ta wadata Jihar Kaduna da abinci da kuma kasa baki daya sakamankon jajircewar da mambobin kungiyar suka yi wajen noman shinkafa.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana rashin jin dadinsa, kan yadda wadansu daga cikin mambobin kungiyar suka kasa cika alkawarin da suka dauka a yayin da suka amince suka karbi bashin tallafin noman shinkafa a Jihar Kaduna.

Alhaji Muhammad Umar Numbu, ya ce kashi 10 cikin 100 ne kacal na wadanda suka amfana da bashin noman shinkafar suka iya biyan bashin a jihar.

Shugaban Kungiyar RIFAN din ya ce da yawa daga cikin manoma sun dauki shirin a matsayin tallafi ne na Shugaban Kasa Buhari, da aka ba su kyauta ba bashi ba.

Ya ce hakan ya sa suke ta wayar da kan ’ya’yan kungiyar nasu don su fahimci yadda shirin yake, domin duk wanda aka ba shi kayan aikin noman shinkafa don ya biya ne a cikin shekara daya.

Alhaji Umar Numbu, ya ce zuwa yanzu shirin ya samu tarnaki a jihar sakamakon ambaliyar ruwa, da kuma matsalar tsaro da aka yi fama da ita a bara. A cewarsa, hakan ya hana manoma da yawa zuwa gona a daminar bara, kuma hakan ya sa da yawa daga cikin manoman suka kasa biyan bashin da suka dauka don noman shinkafa a jihar.

Ya ce wannan ne ya sa suka zauna da Babban Bankin Najeriya (CBN), da Bankin Manoma; inda suka cimma matsaya na su daga wa manoman da a ka bai wa tallafin kafa, zuwa karshen wannan daminar don manoma su kammala biyan bashin.

Ya ce a dalilin haka kungiyarsa ta zauna da babban lauyansu; inda ya ba su shawarwari na su ba manoman takardun tuntuba da tsaida lokaci na maido da bashin kudin da suka amfana da shi.

Shugaban ya shawarci mambobin kungiyar su yi amfani da wannan dama wajen bunkasa noman shinkafa da ciyar da jihar da kuma kasa da abinci a wannan damina.