✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar matasan Arewa ta yi Allah wadai da kiran a saki Sowore

Wata gamayyar kungiyar Matasan Arewa ta fito ta yi Allah wadai da wa’adin da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka bai wa gwamnatin tarayya data…

Wata gamayyar kungiyar Matasan Arewa ta fito ta yi Allah wadai da wa’adin da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka bai wa gwamnatin tarayya data sako Omoyele Sowore wanda jami’an DSS suka kama shi.

A cewar, shugaban kungiyar matasan Kwamrade Muktar Muhammad, a wata zantawa da Aminiya ya bayyana cewa, a maimakon kungiyoyin da suka bada wannan wa’adi ga gwamnati kamata ya yi su yi Allah wadai da abin da shi Soworen ya yi.

An sake kama Sowore, ne kwana daya da bada belinsa bayan ya yi kira da a yi juyin juya hali a kasa.

Hukumar DSS ne ta sake kama shi a harabar Kotun da ke Abuja wanda hakan ya janyo cece kuce a kasa.

” Wannan wa’adi da kungiyoyi ‎masu zaman kansu suke cewa muddin ba’a sake shi ba zasu yi zanga-zanga mai zafi amma fa mu bama goyan bayan wannan mataki na su.”

” Mu ba zamu goyi bayan duk wani abu da zai kawo tashin hankali a kasa ba saboda haka muke yin kira.”

Ya kuma nemi shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da ya sanya baki domin a samu maslaha.