Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

‘Kungiyar Muryar Talaka za ta bude Gidauniyar Marayu’

Daga Hagu Minista Solomon Dalung, Zaidu Bala a tsakiya da Barista Aminu Gamawa
Daga Hagu Minista Solomon Dalung, Zaidu Bala a tsakiya da Barista Aminu Gamawa

Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung, ya ce Kungiyar Muryar Talaka tana shirin bude wata gidauniya ta musamman domin taimaka wa marayu a fadin kasar nan.

Barista Solomon Dalung, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe lokacin taron kungiyar karo na takwas da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta Tarayya FCE (T) da ke Gombe.

ADVERTISEMENT

Ministan ya ce wannan taro ne da suke yi duk shekara sannan kuma na bana musabbabin yinsa a daidai wannan lokaci shi ne don hada kan ’yan Najeriya su zabi shugaba nagari a babban zabe da ke karatowa.

Solomon Dalung, wanda shi ne Uban Kungiyar ya kuma ce a wannan zaben da ke tafe Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kokari wajen gyara siyasar kasar nan daga barin siyasar kudi zuwa siyasar ’yanci, wanda shi ya sa har yanzu ba a fara sayen masu jefa kuri’a ba sannan masu yi din ma ba za su yi nasara ba.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, zaben na ’yanci za a yi kuma kowa nagartarsa ce za ta fitar da shi ba rabewa a jikin wani dan takara ko wata jam’iyya ba, domin ’yan Najeriya sun waye ba za a musu zakin baki ba, za a zabi koma wane ne idan ya cancanta a kuma kowacce jam’iyya yake.

“Ganin ayyukan raya kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a wasu sassan kasar nan musamman ayyukan hanyoyi ya sa yake ganin dacewar a sake zabarsa a bana don ya karasa su ya kuma kara kawo wasu ci gaban a duk fadin Najeriya,” inji shi.

Da yake tsokaci, Shugaban Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Malam Zaidu Bala Kofa Sabuwar Birnin Kebbi, cewa ya yi sun gudanar da taron nasu ne don yin kira a zabi shugaba nagari mai nagarta wanda zai ciyar da Najeriya gaba ba wanda zai mayar da ita baya ba.

Zaidu Bala Kofa Sabuwa, ya ce duk cikin ’yan takarar yana ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya fi cancanta da dacewa a zaba a kan sauran ’yan takarar amma dai ya rage ga ’yan Najeriya su yanke shawara.

Shi ma wani kwararren lauya na kasa da kasa mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum, Barista Aminu Hassan Gamawa, shawara ya bai wa Gwamnatin Tarayya cewa muddin tana son a yi sahihin zabe mai nagarta, to kada ta yi amfani da jami’an tsaro a kan ’yan jam’iyyun adawa.

An ba da lambar yabo ga wadansu da suka yi fice sosai suka kuma ba da gudunmawa a bangaren ci gaban matasa da Najeriya a lokacin taron.