Da Dumi Dumi

Kungiyar Taliban ta yi musayar fursunoni ’yan kasashen yamma guda biyu

Kungiyar Taliban ta saki wasu fursunoni biyu da farkon makon nan, don cika alkawarin da su ka yi a yarjajeniyar musayar fursunoni, wanda ya shafi sakin wasu manyan kwamandojinsu uku.

Majiyoyi masu alaka da kungiyar ’yan ta’addan, sun ce an saki dan Amurka, Kebin King da dan Australiya, Timothy Weeks, a kudancin lardin Kabul. Da King da Weeks, dukkansu Farfesoshi ne a Jami’ar Amurka da ke Kabul, kuma an sace su a watan Agustan 2016 a wajen jami’ar.

Sakin su biyun, ya zo ne ’yan sa’o’i bayan an kai kwamandojin Taliban uku, zuwa Katar domin musayar fursunonin. Fursunonin kungiyar mayakan su uku, sun hada da Anas Hakkani, wanda babban yayansa ne shugaban ƙungiyar ta’addancin, mai alaka da Taliban, wadda ma, ke amfani da sunanta. Anas Hakkani, tare da kwamandojin Taliban, Haji Mali Khan da Hafiz Rashid, tun a shekarar 2014, gwamnatin Afghanistan ke tsare da su.

Musayar ta nuna alamun mika wuya

ADVERTISEMENT

Tabbatar da musayar fursunonin da Shugaba Ashraf Ghani ya yi, bai zo da mamaki ba, sakamakon yadda aka shafe lokaci mai tsawo ana tattauna wa a kai.

A baya, Shugaban ya sha nanata cewa batun sakin mambobin kungiyar Hakkani ba abu ne mai yiwuwa ba, amma a yanzu da wannan musayar, alamu na nuna cewa Shugaban ya sassauto kan kafewar sakamakon yadda yake neman bayar da kai ga Taliban – muddin dai hakan zai share hanyar zama gaba-gadi domin tattaunawar zaman lafiya a kasar.

Amma was una kallon abin ta fuskar wani yunkurin gwamnain Afghanistan din wajen neman zaman lafiya da ta saka batun cikin zaman teburin sulhu inda ya zuwa yanzu aka kawar da batun kafa Gwamnatin Hadin kan Kasa.

Sai dai ko a baya bayan nan ma, kungiyar Taliban din ta fada karara cewa lallai ne dakarun kasashen waje su fice daga kasar – gabanin soma duk wata tattaunawar zaman lafiya tsakanin ’yan kasar Afghanistan. Ko a lokacin ma, Taliban sun ce ba su dauki kasar Afghanistan din a zaman wani bangare na rikicin ko kuma a matsayin gwamnati.

An kai wa sojin Afganistan hari a Kabul

An jikkata mutane biyar sakamakon harin bam da aka kai a wani sansanin soji da ke Kabul, Babban Birnin kasar Afganistan.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan kasar, Nasrat Rahimi, ya fadi cewar wasu da ba a san ko su wanene ba suka ka hari a sansanin soji da ke yanki na 19 a Kabul.

Ya ce sojoji hudu da dan sanda guda sun jikkata, sakamakon harin da aka kai da bama-bamai biyu da aka samar da hannu, ana kuma ci gaba da gudanar da bincike.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin. Sai dai a baya kungiyar ’yan gwagwarmaya ta Taliban ta sha daukar alhakin kai hare-haren bam da dama a cikin kasar ta Afghanistan – tun bayan mamayar da Amurka da kawayenta suka kai, inda suka kifar da gwamnatin Taliban a shekarar 2001.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya