✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyoyi sun bukaci Ganduje ya tsige Sarkin Kano

Wata gamayyar  kungiyoyin farar hula 35, karkashin sunan UMBRELLA OF KANO CONCERNED CIVIL SOCIETY GROUPS ta bukaci Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da ya…

Wata gamayyar  kungiyoyin farar hula 35, karkashin sunan UMBRELLA OF KANO CONCERNED CIVIL SOCIETY GROUPS ta bukaci Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da ya gaggauta fara shirin tsige Sarkin Kano Muhammdu Sanusi II, domin kare doka da oda da kuma ikon da masu zabe na jihar suka ba shi.

Babban Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda suka bukaci hakan a wata wasika da suka aika wa Gwamnan.

Abba Anwar, ya bayyana cewa gamayyar kungiyoyin ta ce tana lura tare da nazarin yadda al’amuran jihar suke kasancewa musamman a wannan lokaci, dangane da dambarwar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar da kuma Sarkin Kanon.

Daga BBC