Da Dumi Dumi

Kurona: An kori Mikel Obi saboda kin buga wa kulob dinsa wasa

Mikel Obi

A  ranar Talatar da ta wuce, kulob din Trabzonspor na Turkiyya ya bayar da sanarwar soke kwantaragin da ya kulla da tsohon Kyaftin din Super Eagles John Obi Mikel saboda kin yi wa kulob din wasa a ranar Lahadin da ta wuce saboda tsoron kamuwa da cutar Kurona.

A ranar Lahadi ce kulob din Tranzaspor ya buga wasan rukunin-rukuni na Turkiyya da kulob din Basaksehir amma yunkurin da kocin Obi ya yi na sanya shi a wasan ya ci tura inda dan kwallon ya ce ba zai buga wasan ba saboda tsoron kamuwa da cutar Kurona da ta addabi duniya.

Tun kafin wasan, an ruwaito Obi yana korafin yadda Turkiyya ta ki dage wasanni a kasar saboda cutar Kurona bayan sauran kasashe a Nahiyar Turai sun dage nasu wasannin.

Game da hakan Obi ya yanke shawarar ba zai yi wasa da rayuwarsa ba ta ci gaba da buga kwallo a wannan lokaci da cutar take ci gaba da mamaye sassan duniya.

Wannan mataki da Obi ya dauka ta sa mahukunta kulob din suka yanke shawarar soke kwantaragin da ke tsakaninsu.

ADVERTISEMENT

Wata sanarwar da kulob din ya fitar a shafin sadarwarsa ta ce:  “Daga yau mun yanke shawarar soke kwantaragin da muka kulla da tsohon Kyaftin din Najeriya John Obi Mikel a ranar 30 ga watan Yunin 2019 wanda zai fara aiki daga ranar 30 ga watan Yunin 2021 saboda kin buga wa kulob din wasa a wannan lokaci.  Tuni John Obi Mikel ya amince da wannan mataki da muka dauka kuma muna shaida wa duniya mun yi rabuwar mutunci.”

Obi dai ya yi wasa a kasashe da dama da suka hada da Norway da Ingila da China da kuma Turkiyya.  Ya shahara ne a lokacin da ya shafe kimanin shekara 10 yana buga kwallo a kulob din Chelsea da ke Ingila.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya