✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwadayin mulki ya sa muka yi mantuwa

Assalamu alaikun da fatan dukan abokan aiki kuna lafiya. Bayan haka ina son a ba ni fili don in bayyana sharhina. Da farko, mu ’yan…

Assalamu alaikun da fatan dukan abokan aiki kuna lafiya. Bayan haka ina son a ba ni fili don in bayyana sharhina. Da farko, mu ’yan Arewa Musulmi da Kiristoci a shekarar 2014, muka roki Ubangiji Ya yi mana sauyi mai amfani Ya yi. Yanzun saboda kwadayin mulki, sai muka manta, za mu zama irin mutanen Annabi Musa, (AS)komai ya yi sai a ce ba a so. To mu guji abin da zai biyo baya. Mu dai Allah Ya taimaki Baba, ya cika alkawarin da ya dauka. Mu addu’armu ke nan gare shi.

Daga Alhassan Baba Manjo 08069738566.

Sakon ban gajiya ga Gizagawa

Salam Edita, don Allah ka isar min da sakona ga dukan GIZAGAWAN Najeriya musamman wadanda suka halarci taron da aka gudanar a Jihar Katsina, Allah Ya huta gajiya Ya kuma kara hada kanmu baki daya.

Daga K. Bello Kiyawa 07032528895

Sakon godiya ga jaridar Aminiya

Assalamu alaikum Edita, don Allah ka ba ni dama domin in mika sakon godiya ga jaridar Aminiya kan irin yadda take bai wa kowa dama ya fadi albarkacin bakinsa ba tare da nuna bambanci ba kamar yadda muke mika sakon gaisuwa. Allah Ya k ara daukaka jaridar Aminiya amin. Sannan Edita don Allah muna rokon a dawo mana da shafin FDK. Daga karshe ina mika sakon gaisuwa ga Mami Hafsat Taraba.  Allah Ya bar zumunci amin.

Daga Shamseeya Idrees Gombe.

Kira ga Kwankwaso

Assalamu alaikum, fatan  alheri  a gare ka  Edita. Ina son in yi kira ga Dokta  Rabi’u  Musa  Kwankwaso  kalubalen  da ke  gabanka  a  Jihar Kano  ya fi  karfin  ka tsai da  surukinka  takarar  Gwamna.Ya kamata ka nemi  mutumin  da  al’ummar  Jihar  Kano  suka  dade  su na  fatan ya zama  Gwamna a jihar,  kamar Al-Amin  Little  ko  Malam Salisu  Sagir  Takai

Daga  G. Sabiyola  Sa’idawa  Gashuwa, 07061636664.

Kira ga dalaget

Salam Edita, ka ba ni dama in yi kira ga dalaget na APC da su yi wa Allah su zaba mana shugabanni nagari a wannan zaben fid da gwani da ke gudana. Daga karshe nake addu’ar Allah Ya ba mu shugabanni nagari amin summa amin.

Daga Sani Mohammed Chindo. Unguwar Karofin Madaki, Bauchi 08030918913.

Zuwa ga Jam’iyyar APC reshen Ningi/Warji

Salam Edita, ka ba ni dama in mika sakona ga Jam’iyyar APC reshen Ningi/Warji. Muna kira ga masu hannu a kan zaben fid da gwani da ke gudana, su yi wa Allah su zaba mana wadanda za su ceto mana yankinmu, kada su zabi son zuciya. Su tuna cewa a baya mun sha wahala, sakamakon gurbatattun shugabanni, Allah Ya sa sakona ya je ga wadanda aka yi dominsu.

Daga Mudassir Maishayi Bakin Tasha, Ningi.  09025297045.

Buhari ikon Allah

Assalamu alaikum Editan Aminiya, da fatan kana lafiya Allah Ya sa haka amin. Ina son in gaya wa masu sukar Baba Buhari cewa lafiya ta Allah ce mu dai sai Baba, in Allah Ya yarda. Buhari ikon Allah.

Daga Yusuf Mai Farar Kasa Bakin K. S. G. Zariya, 08122553362.

Ambaliyar ruwa a Dawakin Kudu

Salam Editan Aminiya, ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Kano da dan Majalisar Wakilai da na jiha masu wakiltar Dawakin Kudu su taimaka wa manoman garuruwan Tsakuwa da Kumburau da Karwai da Gidan Gwangwan da Kyanbo da Daba-Kwari da ruwa ya mamaye gonakinsu a ranar 29/8/2018. Babu wanda ya fita da abin da ya kai mudu biyu amma har yanzu ko karamar hukuma ba ta je ba bare gwamnatin jiha. Talakawa sun shiga matsalar da sai dai su bar shiyyar don neman tsira da kai. Wannan ruwa har yanzu yana nan ba masaka tsinke. Allah Ya ba da ikon taimakawa.

Daga Sani Nababa, Lamba 431 Makau Hotoro B/ KRTB Kano.

Maraba da Sardaunan Kano a APC

Assalam Edita Aminiya, muna yi wa Sardaunan Kano maraba da komowa Jam’iyyar APC da fatan Allah (SWT) Ya kawo mana sauyi mai ma’ana a wannan gwamnati ta Baba Buhari Allah Ya yi mana jagora, amin.

Daga Abdulhameed Uba Shalai tare da Hafsat Gidan Gona Nasarawa, Kano, 09068963651.

Kira ga ‘yan PDP Jihar Zamfara

Assalamu alaikum Edita. Ka ba ni dama in yi kira ga shugabannin Jam’iyyar PDP ta Jihar Zamfara, me ya sa ba za su hada kansu ba su zaba mana dan takarar Gwamna wanda jama’a suke so.

Daga Abdullahi Lawali Gusau.

Sakon jaje ga jama’ar Yobe

Assalamu alaikum, gaisuwa da fatan alheri ga dukan ma’aikatan jaridar Aminiya. Ina son a ba ni dama in mika sakon jajena ga jama’armu ta Jihar Yobe musamman na yankin Zone C wato Yobe ta Arewa sakamakon maida su saniyar ware da Gwamna ya yi wajen fid da dan takarar Gwamna da har yanzu ya sake ba da takara a shiyyarsa. Wannan ya sa muka gane cewa mulkin Jihar Yobe, mulkin kabilanci ne. To shawara a gare ku ’yan Zone C, mu fito kwanmu da kwarkwata mu zabi PDP don mu kawo karshen mulkin kabilanci kada mu zama rakumi da akala mu tashi mu kwatar wa kanmu ’yanci.

Daga Ibrahim 08126461577.

Mun amince da Kwankwaso

Assalmu alaikum Edita, wallahi mun yarda da Kwankwaso wajen amana da cika alkawari. Allah Ya ba ka Najeriya mu ji dadi.

Daga Sayyadi Mai Dansa 08039141455.

Godiya ga Saraki

Assalam alaikum Edita, ina son in isar mana da godiya ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukula Saraki domin ya zo kuma ya taimaka wa mutanen da gobara ta same su a Lafiya. Mun gode, marasa lafiya Allah Ya ba su lafiya, wadanda suka suka rasa rai Allah Ya jikansu, amin.

Daga Bara’u Liman Dabawa.

Kira ga gwamnati a kan bunkasa noma

Salam Aminiya, ina kira ga gwamnati da a bunkasa noman rani da na damina a jihohi da kananan hukumomi a daukacin kasar nan, wanda zai dakushe karfin shaye-shaye da zaman banza da sauran fitinu da suke kunno kai da barazana da jan hankalin dimbin matasan kasar nan. Wadannan abubuwa sun addabi al’umma tare da haifar da koma baya ga tattalin arzikin kasa.

Daga Basiru 08058591624.

Jinjina ga Dallatun Katsina

Assalam Editan jaridar Aminiya mai farin jini ga kowa. A taimaka mini in yabi wanda ya tabbatar da kauyenmu a Jihar Katsina ta hanyar yi mana hanyar da ta dauki sama da shekara 16 ana yi mana karyar za a yi mana gyara a gwamnatin baya. Mu al’ummar Makaurachi da kewaye mun ce gaba dai, gaba dai Baba Masari ikon Allah.

Daga Sagir Garba Sallau Makaurachi 08032810674.

Mu yi hattara matasa

Salam Edita, ka ba ni dama in yi kira ga matasan kasar na cewa mu guji bangar siyasa musamman a zabe mai zuwa don kiyaye mutuncinmu da kuma rayuwarmu da fatan za mu kiyaye.

Daga Ibrahim KSD 08031944943.

Zuwa ga ‘yan Najeriya

Assalamu alaikum Edita. Ka ba ni dama in yi bayani a kan talaucin da ke addabar ’yan Najeriya. Talauci da arziki duk jarrabawa ce daga wurin Allah, sannan zalunci da cin amana suna wurin dan Adam. Babu wani abu wanda za a iya yi wa dan Najeriya ya amfani kowa da kowa. kuma ina yin kira a rage farashin man fetur zuwa Naira 25, ina yi wa shugabanninmu fatan alheri, kamar irin su Bafarawa da sauransu.

Daga Yahaya Tsamaye Gobir 08100346087.

Muna bukatar shafin Dausayin Kauna

Salam Edita, ina son jaridarmu mai albarka Aminiya ta dawo mana da filin Dausayin Kauna (FDK). Dubban mutane na karuwa da sada zumunci a wannan fili, ni ma nasamu aure ta dalilin wannan fili, kuma muna zaune lafiya. Na kasance mai bin labarin Aminiya tun shekarar 2016 har zuwa yau duk Juma’a, don Allah a dawo da filin.

Daga Umar Kano, Sarkin Yakin FDK, Aminiya 07035438533.

Kira ga Gwamna Yari

Assalamu alaikum, ina yi wa Edita fatan alheri. Ina son ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya sani mu Zamfarawa ba dabbobi ba ne da zai kawo mana wani dan takara da ba mu san shi ba, kuma har ya ce ko muna so ko ba mu so shi ne dan takara mu talakawa ba mu da bakin magana.

Daga Shamsu Shehu S.S B.I.P Gusau Unguwar Yarima 08137422269.

 

Kwankwaso ne zai iya takara da Buhari

Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Sanata Walid Jibirin da sauran ’yan Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP su sani ba mai iya kayar da Buhari in ba Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Don haka mu talakawan Najeriya muna kira ga masu son tsayawa takara su yi wa Allah da ManzonSa su hakura su janye su barwa Kwankwaso in har suna so mu kai ga nasara a Jam’iyyar PDP a 2019.

Daga Abdullahi Adamu Damagari, 07062813379

Gwamnati ta kara ma’aikatu

Salam Edita. Ina so in yi amfani da wannan dama in bai wa Gwamnatin Tarayya shawarar ta kirkiro wata ma’aikata da za ta rika kula da biyan kudin wuta da ruwa da sauran bukatu da ma’aikata za su rika ta yadda za rika cirewa daga tushe. Ina ganin haka zai rage yawan yanke wuta da ruwa a ma’aikatun gwamnati.

Daga Garba Ya’u Majiya 08067742692.