✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin Shugaban Kasa ya amince a kafa ’yan sandan Jihohi da na Kananan Hukumomi

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi rahoton kwamitin, sake fasalin rundunar tsaro ta ’yan sanda na mussaman a kan manyan ;aifuffuka, inda suka ba da shawarar…

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi rahoton kwamitin, sake fasalin rundunar tsaro ta ’yan sanda na mussaman a kan manyan ;aifuffuka, inda suka ba da shawarar a kirkiro ’yan sandan jihohi da na kananan hukumomi, domin magance matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

Shugaban kwamitin wanda shi ne Babban Sakataren Hukumar Kare Hakkin Dan adam ta Kasa (NHRC) Mista Tony Ojukwu ya mika rahoton bayan  shugaban kasa ya umarci  Sifeto Janar na ’yan sanda Muhammad Adamu da Babban mai gabatar da kara da su hada kai da hukumar kare hakkin dan adam a kan yadda za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar cikin watanni 3, haka kuma kwamitin ya nemi a inganta tsarin ba da kaso da samar da kayan aikin ga ’yan sandan kasar nan, sannan a  habaka harkar fasahar zamani a rundunar, baya ga hakan a samar da wata cibiya ta bincike na mussaman domin jin korafe korafen al’umma a kan zargin keta hakkin dan adam da cin zarafinsa  a gudanar da aiki da ’yan sanda ke yi.

Kwamitin ya ce kafa irin wannan cibiya zai taimaka  wajen magance irin kalubalen da tsaro ke fuskanta a kasar nan.

Kwamitin kuma ya ba da shawarar korar wasu ’yan sanda 37 a kan laifin cin zarafin hakkin dan adam, a kuma gurfanar da wasu 24 gaban kuliya.

Hakazalika an kuma bukaci Sifeto Janar Muhammad Adamu da ya binciko wasu ’yan sanda 22 da suke da hannu wajen keta hakkokin bani adam kan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba. Sannan kwamitin ya ba da shawarar a biya diyya ga mutane 45 da suka shigar da kokensu, sannan rundunar ta fito karara ta nemi gafarar wadanda aka zalunta.