✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kone katan 146 na bandar kifi a Maiduguri

Hukumar Kwastam ta Kasa a Jihar Borno ta kone katan 146 na  bandar kifi a birnin Maiduguri bayan ta kwace daga hannun wadanda ta kira…

Hukumar Kwastam ta Kasa a Jihar Borno ta kone katan 146 na  bandar kifi a birnin Maiduguri bayan ta kwace daga hannun wadanda ta kira masu fasa kwauri a watan Yunin 2018.

Haka kuma hukumar ta kone sabulun wanka nau’in Crusader  katan 2900, wadanda ta ce an tabbatar da wa’adin yin amfani da su ya shige.

Babban Sufuridantan Hukumar Edeh Bashir ya shaida wa manema labarai a wajen birnin Maiduguri inda aka kone kayan, cewa kifin bai dace a ci ba, haka ma sabulan bai kamata mutum ya yi amfani da su ba.

Hakan yana zuwa ne bayan da Babban Kwantorolan Hukumar Kwastam ta Kasa ya samu korafin cewa manyan siton adana kaya na Hukumar Kwastam a Jihar Borno suna dankare da kayayyakin da wa’adin amfani da su ya kare, kuma bera da sauran kwari suna shiga cikin kwalayen kifi suna ci, wannan ya sa dole a kone su, gudun barkewar cutar zazzabin Lassa.