Da Dumi Dumi

Kyamar baki ko kyamar bakake?

Matakin da bakaken fatar kasar Afirka ta Kudu suka dauka na musguna wa bakake ’yan kasar waje da ke zaune a kasar domin su bar musu kasar tasu ya harzuka mutane da dama a Nahiyar Afirka wanda ya sanya wasu kasashen ciki har da Najeriya umartar jakadunsu da ke kasar su koma gida.

Kyamar bakar fata da al’ummar Afirka ta Kudu suka nuna a kwanakin nan ba shi ne na farko ba, hasali ma dai wannan shi ne karo na uku da suke tayar da kayar baya suna cin mutuncin baki bakaken fata, musamman ’yan Najeriya, domin su bar musu kasarsu, saboda a cewarsu, ’yan Najeriyar sun je kasarsu sun mamaye harkokin kasuwanci sun bar su suna zaman kashe wando.

Bayanin da kafofin yada labarai suke yi cewa bakaken fatar kasar Afirka ta Kudu suna kyamar baki kuskure ne, domin ba duk bakin da ke kasar suke kyamatarsu ba, suna kyamar ’yan uwansu bakaken fata ne da suka fito daga kasashen Afirka, sauran baki fararen fata da kuma wadanda suka fito daga Nahiyar Asiya irin su China da Japan da Indiya da sauransu babu ruwansu da su, ’yan uwansu bakaken fata ne kawai suke jin haushinsu.

Hausawa suna cewa, ‘Idan da amana bai kamata ruwa ya dafa kifi ba.’ Wato idan bakaken fata na Afirka ta Kudu sun san mutunci bai kamata a ce an wayi gari suna ci wa ’yan uwansu bakaken fata da suka fito daga Nahiyar Afirka, musamman ’yan Najeriya mutunci ba, domin su ne suka tashi tsaye waje kwato masu ’yanci daga Turawan mulkin mallaka, amma maimakon su saka musu da alheri sai suna saka masu da tsiya.

Babu irin wulakancin da bakaken fatan Afirka ta Kudu ba su gani ba a wurin fararen fata, wanda ya sanya sauran bakaken fata da ke Nahiyar Afirka suka damu kwarai da cin mutuncin da Turawa ke yi musu, wanda ya sanya a Najeriya baya ga taimakon da gwamnati ke bayarwa, hatta sauran jama’ar kasa sai da suka tara kudi domin taimaka wa bakaken Afirka ta Kudu su samu ’yancin kansu daga Turawan mulkin mallaka, amma abin mamaki a yau wadannan bakaken fatan na Afirka ta Kudu da aka taimaka musu suka samu ’yanci su ne kuma suka juyo suna yakar mutanen da suka taimaka musu.

ADVERTISEMENT

Fararen fatar da suka musguna musu suka kuma bautar da su, suna nan a kasar suna ci gaba da harkokinsu ba tare da wata matsala ba, kuma har yanzu akwai yankuna a kasar Afirka ta Kudu da bakin fata bai isa ya zauna a cikinsu ba. Gaba daya harkokin tattalin arzikin Afirka ta Kudu yana hannun fararen fata ne har yanzu, harkar mulki ne kawai suka sakar wa bakaken fata,  nan ma sai wanda suke so zai zama Shugaban Kasa kuma su ne za su rika juya shi.

Wadanda suka san bakaken fatar Afirka ta Kudu sun bayyana mazansu da cewa ragwage ne, babu abin da suka iya sai tambele, saboda haka suka yi sakaci baki suka fi su kokarin neman arziki, wanda ya sanya matan Afirka ta Kudu suke son hulda da bakake baki, wannan ne ya haddasa kiyayya tsakanin bakake ’yan kasa da bakake baki, domin bakake ’yan kasa suna ganin bai kamata bakaken fata irin su su je kasarsu su fi su iya rawa ba, domin haka suka kafa musu kahon tsana suna so su kore su, amma sun kasa ko nuna yatsa ga fararen fata da suka mamaye komai na kasar suka bar su suna ci gaba da rayuwa a cikin kunci.

Abin da ke faruwa a Afirka ta Kudu darasi ne ga ’yan Najeriya, domin irinsa ne yake faruwa a Najeriya inda wadansu mutane suke nuna kyama ga wadansu ’yan Najeriya suna cewa ba su yarda su zauna a yankunansu ba, sai ga shi su ma ’yan uwansu sun tafi wata kasa ana cin zarafinsu kwatankwacin yadda ’yan uwansu ke musguna wa wadansu a Najeriya.

Ya kamata bakaken fata su farka, su yi kokari su fahimci yadda rayuwa take, domin kuwa bako rahama ne, babu wata kasa ko gari da ke bunkasa sai da baki, duk kasar da take kyamar baki ba za ta taba ci gaba ba. Domin haka Allah Ya tsara, wadansu za su tashi su tafi garin wadansu su zama masu arziki da ake tinkaho da su a garin, su kuma ’yan wannan garin su tafi wani garin su zama hamshakan attajirai. Mafi yawan attajiran da ake da su a duniya ba a garurruwansu ne suka zauna suka samu dukiyar tasu ba, fita suka yi suka je wasu wuraren suka nema kuma Allah Ya taimake su suka samu.

Saboda haka lallai ne mutane su fahimci cewa arziki fita ake yi a nemo shi, ba zama ake yi a gida ya biyo mutum ba, kuma a yayin neman nan ana iya zuwa ko’ina a zauna a duniya har Allah Ya sanya a yi dace.

Ana iya korar baki a rungumi sana’o’in da suka bari amma al’amura su ki tafiya daidai, saboda Allah bai tsara cewa akwai rabon wadanda suka mamaye harkokin bakin mai yawa ba. Saboda haka kyamar baki bakaken fata da ’yan Afirka ke nunawa, kuma su rika girmama baki fararen fata koda suna zaluntarsu ne, ba zai haifar masu da da mai ido ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya