✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyashi ke hana manya taimaka wa matasan ’yan kwallon Arewa – Aliku

Aliku Mustapha Mustapha shi ne Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes ta Jihar Neja, kuma mai tsaron gidan kungiyar ya bayyana wa Aminiya…

Aliku Mustapha Mustapha shi ne Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes ta Jihar Neja, kuma mai tsaron gidan kungiyar ya bayyana wa Aminiya yadda ya fara kwallon kafa da nasarorin da ya samu da burin da yake da shi a  harkar kwallon kafa:

 

Yaushe ka fara buga kwallon kafa?

Na fara buga kwallon kafa tun ina karamin yaro a unguwarmu da kuma a makarantar firamare har ta kai na fara bugawa a matakin ’yan kasa da shekara 13 zuwa lokacin da Allah Ya sanya na fara buga wasa a matakin kwararru.

Ban da Niger Tornadoes ka taba buga wa wata kunkiyar kwallon kafa a ciki ko wajen Najeriya?

A wajen Najeriya dai ban taba buga wa wata kungiya ba, amma a nan Najeriya na buga wa kungiyoyi da dama. A cikinsu akwai Kwara United da Wikki Tourist da Sun Shine da Sharks da sauransu.

Kawo yanzu wadanne nasarori ka samu?

A gaskiya a halin yanzu a harkar kwallon kafa sai dai in yi wa Allah godiya. Domin kuwa Shi ne Yake iya mana ba wai wayonmu ko iyawarmu ba. Don haka zan ce na samu nasarori masu yawa, baya ga cewa kwallon ta kasance sana’ata wacce nake yin duk wasu harkkokina a cikinta gami da taimakon wadansu da suke kusa da ni. Duk da yake ban taba buga wa babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa ba, amma na samu nasarar wakiltar kasata a matakai daban-daban.

Ka ga na buga gasar cin Kofin Duniya ta ’Yan kasa da Shekara 17 wanda aka yi a kasar Finland a 2013 tare da su Michael Obi sannan a 2015 na buga gasar cin Kofin Duniya ta ’Yan kasa da Shekara 20 ita ma mun buga ta tare da su (marigayi) Isaac Promise da kuma Michael Obi din.

Kana da burin buga wa babbar kungiyar kasa ta Super Eagles?

Kwarai kuwa ai wannan shi ne burin duk dan wasa mai buga kwallo a matakin kwararru. Ni ma kuma ina addu’ar Allah Ya ba ni irin wannan dama.

Yaya za ka bayyana yadda ake alkalancin wasanni a kasar nan?

A gaskiya a da ana tafka laifuffuka da kura-kurai wajen alkalancin wasanni, amma yanzu zan iya cewa an samu ci gaba sosai ganin yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ta dage a kan daukar matakan ladabtar da masu yin irin wadannan laifuffuka.

Yaya ka ji sa’ar da kungiyar  Kano Pillars ta doke ku a wasan karshe na gasar cin Kofin Kalubale ta Kasa?

Abin bai yi mini dadi ba ko kadan. Amma idan ka dubi yadda kungiyoyi wajen 100 suka fafata har muka samu damar kaiwa ga wasan karshe, to kuwa dole za ka yaba wa Niger Tonadoes. Sannan wani abu shi ne yadda Kano Pillars a matsayinsu na wadanda ake ganin kamar sun fi mu manyan ’yan wasa suka kasa cire mu har sai da ka kai fagen bugun finareti shi ma abin jin dadi ne.

Wadanne kalubale ’yan kwallo daga Arewa suke fuskanta?

Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne na wadanda za su tallafa mana wajen fita waje. Ba kamar ’yan wasan Kudu ba wadanda suke samun tagomashi wajen masu daukar nauyinsu zuwa kasashen waje don neman kungiyoyin da za su bugawa. A nan Arewa akwai kyashi, mutanenmu suna ganin idan suka taimaka maka ka zama wani za ka yi kafada-da-kafada da su. Su a kullum so suke yi ka zauna a karkashinsu kana yin maula. Don haka ya kamata masu hannu da shuni su farka daga barci su san wannan harka ce ta kasuwanci mai kawo kudi, kai ka samu sannan wanda ka taimaka masa ma ya samu, su daina hangen in sun kai mutum ya haye me zai faru?

Wannan shi ne ma ke sanyawa babu ’yan wasan Arewa sosai a babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa. Domin babu masu karfafa mana gwiwa, sannan sau da dama ana kiran ’yan wasan da suke wasa ne a waje a matakin babbar kungiyar ta kasa.

Mece ce fatarka a kakar wasa ta bana da za a fara?

To ina rokon Allah Ya dafa mana kuma Ya ba mu sa’a mu wuce matakin da muka gama da shi a kakar da ta gabata. Kuma ina sa ran za mu yi kokari sosai.