Search
Subscribe
Labarin Aku

Labarin Aku

Assalamu alaikum Manyan Gobe  tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku Labarin Aku. Labarin ya yi nuni ne kan yadda amfani da kakkausar lafazi ke jawo wa mutum fadawa cikin halin kunci. A sha karatu lafiya.

Taku: Amina Abdullahi

Akwai wani Aku wanda ke zaune a wani daji. Akun yana da ’ya’ya biyu inda da zarar gari ya waye zai yi sammako ya tafi nemo musu abinci. Sannan bayan ya nemo sai ya fita yawo sai gab da magariba yake dawowa.

Ran nan bayan ya fita nemo wa ’ya’yan  abinci kamar yadda ya saba, bayan ’yan mintuna sai wani maharbi ya kwashe masa ’ya’ya ya kai gidansa.

Sai dai an yi rashin sa’a ’ya’yan maharbin ba su da tarbiyya don haka suke sakin kowace irin magana a kowane lokaci ba tare da sun yi taka -tsantsan ba.

Wata rana sai daya daga cikin ’ya’yan Akun da maharbi ya kai gidansa ya gudu, kuma bai zame ko’ina ba sai gidan wani Sarki.

Shi ko dayan da bai samu kubuta ba sai ya koyi kakkausar lafazi kasancewar zamansa da ’ya’yan maharbin.

Wata rana sai wata mayya ta kawo ziyara gidan maharbi. Akun daga jin sallamarta sai ya shiga zaginta yana fada mata bakaken maganganu. Saboda haushi sai mayyar ta yi wuf ta shake masa wuya sai da ya mutu.

Mu kwanan nan.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin