✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladi Adebutu, ya caccaki shugbannin majalisu a kan gyaran majalisa

“Tsohon Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya, Ladi Adebutu, wanda ya taba wakiltar mazabar Remo, ya bayyana cewa ana murnar cewa an samu Shugabannin Majalisar Dattawa…

“Tsohon Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya, Ladi Adebutu, wanda ya taba wakiltar mazabar Remo, ya bayyana cewa ana murnar cewa an samu Shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai, Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila a matsayin masu kyakkyawar manufa amma kuma a halin yanzu yanzu suna neman zama karfen kafa ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya fadi haka ne a garin  Abeokuta, na Jihar Ogun a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani bukin cikar shekara da wani bangare na Jam’iyyar PDP ta jihar ta shirya.

Adebutu, wanda ya tsaya takarar gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata na 2019, ya kuma ba majalisun sabon lakabi, wanda ya kira da wani sashe na Jam’iyyar APC mai mulki.

Tsohon Dan Majalisar ya kuma kira shuganannin majalisun na Tarayya, Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila da suna ’yan amshin shata, wanda ya bayyana yadda suke aiki a matsayin wani tushe na ruguza siyasa.

Adebutu har walau ya yi tir da yadda kasar nan take kara fadawa cikin matsalar bashi, abin da ya ce abin takaici ne ainun.

A wata sabuwa kuma shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC, sun lullube wa ’yan Najeriya kura da fatar tunkiya, wanda ya ce kuma asirin hakan zai tonu ne a cikin shekara ta 2020.

Secondus ya fadi haka ne ta bakin babban mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Ike Abonyi, a wani sako na sabuwar shekara da ya aika wa ’yan Najeriya a ranar Talata da ta gabata, wanda a ciki ya kira gwamnati mai ci da suna “gwamnatin kama karya”.

Shugaban na PDP ya bayyana cewa an danne sashen shara’a na kasa yayin da su kuma ’yan majalisu suka zama ’yan amshin Shata ga sashen zartarwa. Ya kuma bayyana cewa ana takura ma ’yan jarida kuma ana ci gaba da cin mutuncin ’yan adawa, inda ya bayyana cewa wannan karfa-karfa ce da salon kama-karya da sunan damokuradiyya.

Ya bayyana cewa 2020 shekara ce da za ta zama ’yan Najeriya za su kara shiga sabon kangi duba da yadda ’yan majalisun suka amince wa sashen zartaswa su sake ciwo sabon bashi mai dan karen ruwa daga kasashen waje.

Shugaban na jam’iyyar ta adawa, ya bayyana cewa 2020 abubuwa za su kara rincabewa, duba da yadda ake zargin harkokin cin hanci da rashawa na kara samun tagomashi a karkashin wannan gwamnati ta yadda ake ta gabatar da zarge-zarge na cin hanci da rashawa a kan wasu kusoshin gwamnati.

“Wani dadin-dadawa kuma shi ne yadda hada-hadar bangaren man fetur ta kasa ta kazance sannan kuma ga wasu ma’aikatun gwamnati sun zama wani tsani na salwantar da kudaden jama’a.” inji Secondus.

Da yake sharhi game da shekarar da ta gabata, Secondus ya bayyana shekara 2019 a matsayin ma fi tsanani a tarihin siyasar Najeriya. Ya ce an banzatar da damokuradiyya aka kuma ba wa wasu abubuwa da ka iya barazana ga damokuradiyyar karfi a karkashin jagorancin jam’iyyar APC a wannan kasa.

Don haka Secondus ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar nan, musamman ma kafafen yada labarai da kungiyoyi da su bude idanuwansu a kan wasu shirye shirye na gwamnati da ya kira wadanda ba za su haifa wa kasar da mai ido ba.