Search
Subscribe
Ladubban zabar mijin aure (2)

Ladubban zabar mijin aure (2)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fata Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladubban da mace Musulma za ta yi amfani da su wajen zabar mijin aure, inda za mu karasa bayani kan ladubban lokacin jiran fitowar miji mafi dacewa. Da fata Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin:

Ladabi na 5:

Kyautata halayya:

Lokacin jiran fitowar miji, yana daga cikin abu mafi dacewa ga mace Musulma ta kasance mai kyautata halayyarta ta kowane fanni na rayuwa, wannan zai kawo mata kwarjini, farin jini da kuma dacewa da miji mai kyakykyawan hali. ’Yar uwa za ta yi haka ne ta wadannan hanyoyi:

Kyautata halayyarta wajen yadda take mu’amula da mutane, domin mutane su ne shaida, duk yadda zuciyarki ke da kyau, duk irin yadda kike riko da addini, in babu kyakykyawar mu’amala tsakaninki da mutane, to mafi yawan mutane ba za su yi la’akari da riko da addininki ko kyan zuciyarki ba, za su shaide ki da abin da suka sani na yadda kika mu’amulance su. Misali, in ba ki kyautata mu’amularki da su, to za su shaide ki da girman kai, rashin sanin mutuncin mutane, wulakanci da sauransu. Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Mafi alherin cikinku shi ne mai kyawun halaye da dabi’u.”

Don haka ya ’yar uwa! Sai ki zama mai saukaka mu’amularki da mutane ta hanyar yawan kyautata musu, gaisuwa mai kyau cikin fara’a ga duk wanda ya dace ki gaida; kawar da kai ga rashin kyautatawar mutane; wasa da dariya ga wadanda suka dace ki yi irin haka da su, kamar kawaye da ’yan uwa da sauran kyawawan ayyuka da suka dace da kyakykyawar mu’amala.

Kamun kai:

Kamun kai na nufin mutum ya kasance yana mulkar zuciyarsa ta yadda bai biye wa soye-soyen zuciyarsa wajen yin abubuwan da ba su dace ba. Ya ’yar uwa! Ki sani, babu yadda za a yi ki zama mai kamun kai sai in kawayen da kike tare da su sun zama masu kamun kai, in kuwa  ba su da kamun kai, kuma kika ci gaba da kawance da su, to dole ne ki wayi gari ba ki da kamun kai. Domin Manzon Allah (SAW) ya ce mutum yana a kan addinin da abokansa suke.

Haka kuma za ki iya kyautata halayyarki ta hanyar barin duk wasu dabi’u marasa kyau da ba su dace da duk wata macen kirki ba: kamar yawan yawace-yawace cikin unguwa; yawan yin rigima ko fadace-fadace da mutane; yawan fadar magana da habaici ga mutane; yin abokai maza da tsayawa ana hira a kan hanya tare da su; yawan cin bashi; yin kawaye da marasa tarbiyya da kamun kai; dabi’un nuna isa, jiji-da-kai, takama, bagu da jin ni na fi kowa da sauransu.

Ladabi da biyayya:

Wadannan sinadarai biyu suna da matukar muhimmanci wajen haskaka kyawun halayyar ’ya mace; duk yadda kike ganin kina da kyan hali, matukar ji da kai da takama na sa ba ki iya yin ladabi da biyayya ga iyaye, malamai da sauran magabatan da ya dace a bi su sau-da-kafa ba, to wannan rashin ladabi zai lullube sauran kyawawan halayenki har ma ba za a gan su ba. Kuma ki sani, mafi yawan maza suna kwadayin samun mace mai ladabi da biyayya domin wannan dabi’a ce da ke samar da zama mai sauki kuma mai dorewa a tsakanin ma’aurata.

Sai mao na gaba sauran bayani na zuwa Insha Allah, da fata Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin