Da Dumi Dumi

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin Tambayoyi

Yarinyar da aka ce kirjinta ba ya girma saboda watakila matsalolin sinadaran hormones to shin irinsu za su iya daukar juna biyu?

Daga Ali, Kano

Amsa: Eh, kwarai kuwa in dai tana al’ada lami lafiya za ta iya daukar ciki. To yara nawa ne kanana ba su da wasu alamun girma kawai idan aka yi sake sai dai a gansu da juna biyu. Ai in dai matsalar ba ta shafi yanayin al’ada ba, tsaf za ta iya samun juna biyu. Kai yawancinsu ma za ka sha mamaki da sun samu juna biyu jikinsu ke fara samar da wadancan sinadarai na hormones da suka rasa, nan da nan kafin wata tara yarinya ta zama kamar babba

 

ADVERTISEMENT

Wadanne alamomi ne za a iya gani a yi saurin gane mai juna biyu wadda ba ta jima da aure ba?

Daga Malama Mai Tambaya

Amsa: A’a haba ai ku za a tambaya wannan. Ku mata ku za a tambaya, domin kafin likita ya ganta ku kuke tasa keyarta a je asibiti saboda ku ma kuna shakka. Duk alamun da ake gani ai a jikinku yake don haka kun san su sarai. Kawai mu a asibiti gwaji muke mu tabbatar da shigar cikin. Kuma kayan gwajin yanzu ko a kyamis za ki iya samu.

 

Ina fama da matsalar al’ada ce, sai ta zo wannan wata sai kuma ta yi kamar wata uku kafin ta sake zuwa. Shin wannan matsala ce?

Daga Zaina Janyau

Amsa: Eh, kwarai matsala ce.

 

Shin yaro namiji zai iya girma ne a shekara 10? Domin dan yayata da kadan ya wuce 10 amma duk alamun girma sun nuna a jikinsa

Daga Al-Ameen Yabo

Amsa: Eh kwarai kuwa ana samun irin wannan a maza da mata, amma sai daidaiku. Mata ma sun fi samu fiye da maza, kamar yadda muka fada a sama. Kawai ana tunanin yarinya kamar karama ce a shekaru sai dai a ga alamun girma sun cika. A likitance muna kiransa precocious puberty, wato kamar dai a ce saurin girma. Amma ba wata matsala, wato ba wani ciwo ba ne, kawai dai za a ga yaran a jiki kamar babba amma daga kiyasin hankalinsu an san yara ne. Akwai su. Kai yanzu ma a wannan zamani saboda yawan kayan ciye-ciye ba irin na da ba ne abin ma kamar ya karu.

 

Yaro ne ya tashi da safe wuyansa wajen muka-muki a kumbure, bayan kwana biyu kuma sai kanensa ya tashi da kumburin shi ma. Ko matsala ce?

Daga Shehu JK, Funtuwa

Amsa: Eh, da alama matsala ce domin ciwon ya yi kama da ciwon mumps wato ciwon hangum. Wata kwayar birus ce ke kama muka-mukin yara wadanda ba a musu allurar rigakafin hangum ta MMR (alluran hangum da bakon dauro da agalawa) a wata daya da rabi da na shida ba. Watakila ke nan ma ba a wa yaran wannan allurai ba. In dai haka ne kuwa ka ba da Katsinawa, koda yake su ma suna cewa ku ba nasu ba ne. Illar wannan kwayar cuta ita ce tana iya shiga ’ya’yan maraina ta nakasa su. A yanzu dai ba magani. Idan akwai yaran da ba ka yi wa wadannan allurai ba, koda sun kamu ka je a yi musu.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya