Da Dumi Dumi

Laifin fitar da fim ba tare da an tace ba: An daure Furodusa Sani Rainbow

Furodusa Sani RainbowA Juma’ar da ta gabata ne Kotun tafi da gidanka da ke karkashin hukumar tace-tace fina-finai ta Jihar Kano ta yanke wa shahararren furodusa Sani Rambo daurin wata uku ko tarar dubu 30 bisa laifin fitar da fim din ‘Kicimilli’ ba tare da hukumar ta tace shi ba.
Alkalin kotun Mukhtar Ahmed ne ya yanke hukuncin inda ya ce furodusa Sani Rainbow ya fitar da fim din ‘Kicimilli’ ba tare da ya kawo hukumar tace fina-finai ta tace shi ba, wanda haka ya saba wa sashi na 97 na hukumar da aka yi a shekarar 2001, kuma hakan babban laifi ne kamar yadda sashi na 112 na hukumar ya bayyana. Saboda haka ne hotun ta yanke masa daurin shekara daya ko kuma tarar dubu 70.
Daga baya ne kotun ta yi masa sassauci inda ta yanke masa daurin wata uku ko kuma tarar dubu 30, inda kuma ya biya tarar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya