✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lalong ya koka kan kankantar alamomin jam’iyyu da ke jikin kuri’u

Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya koka kan yadda alamomin jam’iyyu suka kasance kanana a jikin kuri’u na Shugaban kasa da na majalisun tarayya.…

Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya koka kan yadda alamomin jam’iyyu suka kasance kanana a jikin kuri’u na Shugaban kasa da na majalisun tarayya.

Gwamna Lalong ya yi korafin ne bayan ya kaxa quri’a a Makarantar firamare ta LGEA da ke kauyen Ajikamai a Karamar Hukumar Shendam a yau Asabar.

Gwamnan ya ce sai da ya kalli kuri’arsa sau uku kafin ya tabbatar da cewa ya zabi jam’iyyarsa.

Ya ce, “Akwai babban kalubale dangane da takardar kuri’u, na dauki lokaci kafin na gano alamar jam’iyyata. Na kalla kusan sau biyu zuwa uku kafin na gano jam’iyyata, “Ina kira ga INEC cewa nan gaba su qara wa alamomin jam’iyyun girma don masu zabe su iya tantancen jam’iyyun da suke so su zava cikin sauki.” In ji Lalong.

Lalong ya kuma yaba wa al’ummar Filato kan yadda suka fito don kada kuri’arsu.