✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lalong ya nuna farin ciki da goyon bayan da Musulmin Filato suke ba shi

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya nuna farin cikinsa  kan goyon bayan da al’ummar Musulmin Jihar suke bai wa gwamnatinsa. Gwamna Lalon ya nuna farin…

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya nuna farin cikinsa  kan goyon bayan da al’ummar Musulmin Jihar suke bai wa gwamnatinsa.

Gwamna Lalon ya nuna farin cikinsa ne lokacin da ayarin shugabannin al’ummar Musulmin jihar, suka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a gidan gwamnatin jihar da ke garin Jos.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmin su ci gaba da bai wa gwamnatinsa goyon baya kan kokarin da take yi, na ganin an samu dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali, a kowane bangare na jihar.

Har ila yau ya yi kira ga al’ummar Musulmin su ci gaba da ba shi goyon baya da hadin kai domin ganin gwamnatinsa ta samu nasara, kan kudirorin bunkasa jihar da ta sanya a gaba.

Gwamnan wanda Mataimakinsa Farfesa Sonnie Tyoden ya wakilta, ya bai wa al’ummar Musulmin tabbacin cewa gwamnatinsa a shirye take ta ci gaba da daukar tsauraran matakai  kan miyagun da suke garkuwa da mutane da kai hare- hare ga al’ummar jihar.

Ya ce a wannan wa’adi na biyu na gwamnatinsa, al’ummar jihar za su ga ayyukan ci gaba a dukkan kananan hukumomin jihar, tare da dukkan wuraren da al’ummar Musulmi suke a jihar.

Daga nan ya yaba wa al’ummar Musulmin kan yadda suka fito kwansu da kwarkwatarsu a zaben da ya gabata suka zabe shi, tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A jawabin jagoran ayarin Musulmin, Mai martaba Sarkin Wase Alhaji Muhammadu Sambo Haruna ya ce sun kai wa Gwamnan ziyarar gaisuwar Sallar ce kamar yadda suka saba yi a kowace shekara.

Ya ce al’ummar Musulmin jihar masu son zaman lafiya da bin doka ne, kamar yadda addininsu na Musulunci ya koyar. Ya bai wa Gwamnan tabbacin cewa al’ummar Musulmin za su ci gaba da bai wa gwamnatinsa goyon baya da hadin kai, domin ganin ta samu nasara a dukkan kudirorin da ta sanya a gaba.

Ya yi kira ga Gwamnan ya ci gaba da kokarin da yake yi wajen ganin an magance matsalolin tsaro a jihar.

Har ila yau ya yi kira ga Gwamnan ya yi kokari ya ga an sake gina Babbar Kasuwar Jos.