✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lampard ne zai horar da Chelsea – Harry Redknapp

Tsohon kocin kulob din Tottenham da ke Ingila Hary Redknapp ya yi hasashen tsohon kyaftin din Chelsea, Frank Lampard ne zai zama kocin kulob din…

Tsohon kocin kulob din Tottenham da ke Ingila Hary Redknapp ya yi hasashen tsohon kyaftin din Chelsea, Frank Lampard ne zai zama kocin kulob din kafin a fara kaka mai zuwa.

Redknapp wanda ya horar da kulob da dama a Ingila da suka hada da Tottenham da Postmouth da Kueens Park Rangers da Southampton da kuma West Ham United ya ce a ra’ayinsa babu wanda ya fi dacewa ya zama kocin Chelsea fiye da Lampard.

Ya fadi haka ne a shekaranjiya Laraba lokacin da yake hira da kafar watsa labaran wasanni ta BBC Radio 5 libe.

Frank Lampard dai ya lashe Kofin Firimiya sau uku da Kofin Zakarun Turai sau daya a lokacin da yake yin kwallo a Chelsea.

Bayan ya yi ritaya  sai ya koma kocin kulob din Derby County da ke buga gasar rukunin ’yan dagaji a Ingila a bara, kuma alamu sun nuna zai maye gurbin tsohon kocin Chelsea Sarri da ya canja sheka zuwa kulob din Jubentus a makon jiya.

Yanzu haka Lampard yana  da shekara 40.