✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lauya ta mutu bayan ta tona asirin makauniyar bogi

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Jihar Ekiti ta bayar da labarin mutuwar shugabar kungiyarsu ta bangaren mata ta jihar, Misis Oluseyi Ojo. Marigayiyar ta…

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Jihar Ekiti ta bayar da labarin mutuwar shugabar kungiyarsu ta bangaren mata ta jihar, Misis Oluseyi Ojo. Marigayiyar ta mutu ne bayan ta bayar da labarin tona asirin wata mata mai suna Nzube Ekene da ke yawon barace-barace a kan hanyoyi a matsayin makauniya, alhali tana gani da idonta duk biyun.

Dan takarar kujerar shugabancin Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) a zabe mai zuwa Barista Dele Adesina (SAN) shi ne ya tabbatar da mutuwar wannan mata a ranar Alhamis ta makon jiya. Kafin asirin Nzube Ekene makauniyar bogi ya tonu ta saba fita sanye da tabarau a fuskarta da daya daga cikin ’ya’yanta biyu mai shekara 10 take yi mata jagora zuwa kan hanyar shataletalen babban titin Fajuyi a Ekiti a inda fitilar bayar da umarni ababen hawa (traffic light) take tsayar da abubuwan hawa da ta saba yin amfani da irin wannan dama wajen rokon kudi ga masu motoci.

Marigayiya Oluseyi Ojo, ce ta bankado sirrin wannan mata da ’yan sanda suka hanzarta kama ta da aka sanya mata ankwa a hannaye tare da ingiza keyarta zuwa hedkwatar ’yan sanda a garin Ekiti domin ci gaba da binciken al’amarin. Mutuwar Lauya Oluseyi Ojo, ya razana wasu mutane masu hasashen cewa, makauniyar bogi Nzube Ekene, ce ta kama kurwarta.

Sai dai sanannen Lauya, Dele Adesina (SAN), wanda ya bayar da labarin mutuwar matar ya yi watsi da wannan batu a inda ya ce “A yau Seyi ta tafi ta bar mu bayan fama da cutar sikila na tsawon shekaru 35 da tayi.

Ta bar mu a daidai lokacin da muke gudanar da bikin raba kyautuka ga mabukata domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.”

Bincike ya tabbatar da cewa makauniyar bogi Nzube Ekene da ’yarta mai yi mata jagorar karya suna can a hannun ’yan sanda ana binciken lamarinta.