Search
Subscribe
Lemon Frooty Happy Hour ya sake samun yabo daga jama’a

Lemon Frooty Happy Hour ya sake samun yabo daga jama’a

Masu amfani da lemon kwalba na Frooty Happy Hour Chibita, sun bayyana gamsuwa da sabon fakitin da Kamfanin Chibita ya fito da shi wanda a yanzu ana samunsa a farashin Naira 25 a kowane karamin fakiti.

Wani dan jarida mazaunin Legas, Mista Joseph Uju, ya bayyana gamsuwarsa da sabon fakitin na Frooty Happy Hour, wajen sanya nishadi da gamsarwa da kuma dandano mai dadi.

Ya ce lemon wanda ake samunsa a farashin Naira 25, yana samar da yanayin da zai dace da kasuwa.

“Lemon Frooty Happy Hour na Kamfanin Chibita ya zo min da ’ya’yan itatuwa da suke da dadi ta hanyar dandano mai gamsarwa da sanya annashuwa. Yana da saukin saye yana a cikin mazubi milimita 100 da ke ba ni damar tafiya da shi wajen aikina domin samun nishadi,” inji shi.

Shi kuwa Machael Bosun, da yake sana’ar yin zayyana “graphic” a Ilupeju, ya yaba wa lemon Frooty Happy Hour na Kamfanin Chibita ne kan yadda lemon ya kasance mai tsabta kuma mai saukin saye da kuma sanya nishadi mai gamsarwa.

“Tun lokacin da na sha lemon Frooty Happy Hour na samu gamsuwa ta hanyar canja min tsarin rayuwa, kuma a bayyane yake da ’ya’yan itatuwa na asali kuma ana samun nishadi daga gare shi. A yanzu ina iya samunsa a mazubin da za a iya rikewa a hannu kuma in sha a duk rana,” inji Eteng.

Da yake bayani lokacin taron jin ra’ayin abokan hulda Daraktan Kamfanin Mista Probal Bhattacharya, ya ce amsar da muke samu daga abokan huldarmu ya nuna cewa kamfaninmu ya zama jagaba a bangaren kirkira da samar da farashin da yake dacewa a bangaren masana’antar lemo. Ya ce samun lemon Frooty a farashi mai rahusa ya kara habaka samar da sabtataccen a bin sha a kasuwa.

“Muna yunkurin samar wa abokan huldarmu a Najeriya  hanyar samun rayuwa mai inganci ta hanyar samar musu abin sha mai tsabta kuma mai dandano mai gamsarwa,” inji shi.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin