✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likita ya yi wa mutum 30 tiyata kyauta saboda murnar zaben Buhari

Wani likita mai zaman kansa mai suna Dokta Abayomi Waheed ya cika alkawarin da ya yi na yi wa marasa lafiya talatin aikin tiyata kyauta…

Wani likita mai zaman kansa mai suna Dokta Abayomi Waheed ya cika alkawarin da ya yi na yi wa marasa lafiya talatin aikin tiyata kyauta idan Shugaba Buhari ya ci zaben bana.

Kafin babban zaben bana, Dokta Waheed wanda ke aiki a asibitinsa na Crest da ke Igando a Legas ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa ya yi alkawarin idan Shugaba Buhari ya ci zabe zai yi wa marasa lafiya 30 aikin tiyata kyauta a cikin kwana 30 wato kowace rana mutum daya.

Wakilin Aminiya ya bibiyi alwashin da Dokta Abayomi Waheed ya yi inda ya ziyarci asibintin na Crest  a Unguwar Igando a rana ta 21 da fara yi wa marasa lafiyar aiki kyauta wato ranar Laraba makon jiya inda ya tarar da marasa lafiya da dama da suka amfana da aikin tiyatar.Wadansu an yi musu aikin kaba, wadansu an yi masu aikin cire tsakuwar ciki (afendis) da sauransu.

Wata dattijuwa mai suna Fausat Yusuf da ta amfana da aikin ta shaida wa Aminiya cewa ’yarta ce ke amfani da asibitin na Crest ita ce ta samu labarin cewa likitan yana yi wa marasa lafiya aiki kyauta don haka ta sanar mata ita ma ta zo aka yi mata aiki. “A baya na yi fama da ciwon kaba, inda na yi amfani da magani iri-iri na asibiti da na gargajiya mun kashe kudi masu yawa kafin mu zo nan, ko da na zo aka binciki lafiyata sai aka yi min aiki, kuma ba a karbi ko sisi ba. Sun fada mana cewa sun yi mana aikin kyauta ne saboda murnar nasarar da Shugaba Buhari ya yi a zaben bana. Mun gode Allah kwarai a yanzu na samu lafiya, ina fatan ragowar likitocin kasar nan su yi koyi domin talakawa su amfana,” inji ta.

Ita ma Temitayo Gbadebo mai kimanin shekara 40 ta shaida wa Aminiya cewa daga Jihar Ogun ta zo bayan wani da ya ji labarin ya sanar da ita. Ta ce ta fi shekara 3 tana fama da wani kari da ya fito mata a kirji a daidai kasan mamanta, yake kuma kumbura.

Shi ma wani mutum mai suna Rafel Nwobe dan asalin Jihar Abiya mai kimanin shekara 55 da aka yi wa aikin fitar da tsakuwar ciki ya shaida wa Aminiya cewa yana aiki da wani kamfani ne a matsayin mai gadi. Ya ce manyan jami’an kamfanin ne suka sanar masa cewa ya je asibitin domin ana yin aiki kyauta. Ya ce sun turo masa sako ne ta wayar salula.

Da wakililinmu ya tambaye shi ko ya san dalilin da ya sa aka yi masa aikin kyautar, sai ya ce, “Ba su fada min dalilin ba ni na dauka gwamnati ce ta ce a yi mana aikin kyauta,” inji shi. Wakilinmu ya fada masa saboda nasarar Buhari likitan ya yi musu aikin kyauta inda ya tambaye shi ko Shugaba Buhari ya cancanci a yi masa wannan karamci? Sai ya ce bai cancanta ba, “Duk da dai ni ban yi zabe ba, sakamakon batan katin zabena, amma Shugaba Buhari bai cancanci a yi masa wannan alwashi ba, koda yake albarkacinsa ne aka yi mana aikin kyauta, ni ban dade da fara aiki ba, shi ya sa ban iya tara kudin da zan biya a yi min tiyatar ba, amma na gode Allah da Dokta Waheed ya yi min aikin kyauta,” inji shi.

Wata mata mai suna Misis Fabiyi ta shaida wa Aminiya cewa fiye da shekara biyu take fama da lalura ta ce a baya ta je asibiti likita ya ce sai ta ba da Naira dubu 70 a yi mata aiki.

Wadansu iyaye da suka zo da dansu don a yi masa aikin kaba, mahaifiyarsa mai suna Folake Hamzat ta ce zuwa yanzu yaron ya cika shekara 6 kuma a baya sun jarraba magungunan asibiti da na gargajiya sai ga shi yanzu sun zo kuma za a yi wa yaron aiki kyauta, “Ina fatan ya samu sauki.”

Dokta Abayomi Waheed ya shaida wa Aminiya cewa ya dade yana matukar kaunar Shugaba Buhari tare da fatan Allah Ya ba shi jagorancin kasar nan da kuma yi masa addu’ar samun nasara, “Tun lokacin da yake mulkin soji nake jin ana fadar gaskiyarsa da rikon amana, dabi’un nan nasa ne suka sanya kaunarsa a zuciyata, ina da tabbacin mutum ne da ke da kyakyawar manufa ga kasar nan, don haka na yi alwashin in har Allah Ya ba shi nasara a zaben bana zan yi wa marasa lafiya 30 aikin tiyata kyauta kowace rana mutum guda,” inji shi

Dokta Waheed ya ce fatarsa ita ce abokan aikinsa likitoci su yi koyi da irin wannan aiki domin amfanuwar al’umma.