✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Limamin da ya ceci Kiristoci 300 ya gana da Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya karbi bakoncin limamin masallacin da ya ceci Kiristoci 300 mai suna Imam Abdullahi Abubakar, wanda ke da shekaru 83.…

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya karbi bakoncin limamin masallacin da ya ceci Kiristoci 300 mai suna Imam Abdullahi Abubakar, wanda ke da shekaru 83.

Mataimakin shugaban Najeriya ya ce, wannan limami ya cancanci lambar yabo saboda irin kokarinsa na ceton rayuwar Kiristo ta hanyar samar masu mafaka  a cikin masallaci. Sakamakon harin ‘yan bindgar da suka shiga garuruwan Yelwan Gindi Akwati da Swei da kauyen Nghar duk a karamar hukumar Barkin Ladi jihar Filato a shekarar bara.

Osinbajo, ya karbi bakoncin Limamin da mai unguwar Damafulul Mangai da wasu ayarin shugabannin unguwar.