✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mabambantan sakonni daga fadar FDk

Sakon ta’aziyya FDk, don Allah ka mika sokona ga Dokta Muhammad Shafi’i Sankalawa bisa rasuwar da masoyiyarsa, A’isha Muhammad Sankalawa. Allah Ya jikanta da rahama,…

Sakon ta’aziyya

FDk, don Allah ka mika sokona ga Dokta Muhammad Shafi’i Sankalawa bisa rasuwar da masoyiyarsa, A’isha Muhammad Sankalawa. Allah Ya jikanta da rahama, amin.

Nusaiba Abdullahi Sankalawa, 07037137431

 

Fatan Alheri

Dausayin kauna, ina yi maku fatan alheri, fatan kuna lafiya. Wannan ne shigowata ta farko cikin filin nan namu na ma masoya. Fatan alheri, da fatan Allah Ya kara dankôn soyayya, amin.

Daga Bilkeesu Muhammad Kaduna

 

Kishi shirmen mata

FDk, Allah saka maka da alheri amma akwai aiki gabanka. Ko ka san kishi kumallon mata ne amma a da, yanzu kishi ya zama shirmen mata? Don akwai sahihan labarai masu tsoratarwa kan yadda mata ke nakasa mazajensu, wani sa’in har da kisa, don kawai miji zai kara aure. FDk, kada ka gaji, ka ci gaba da fadakar da matasa mata kan abin da ake yi in miji zai kara aure da yadda ake zama da kishiya don samun rayuwar aure mai albarka. Mata ku sani, babu illa ga auren mace fiye da daya muddin mijin zai yi adalci.

Daga Amiru Isa Bakori, 07068147933

 

Labarin Farida

FDk, barkanka da warhaka, fatan alheri gare ka, da fatan kowa lafiya, ya jama’a? Gaskiya labarin Kishi Kumallon Mata na Farida labara ne mai dauke da darussa na rayuwa iri-iri saboda akwai malaman da ba su da tarbiyya, wadanda duk kokarin daliba in dai ta kama kanta, ta ki ba su damar su yi lalata da ita, to ba za su ba ta sakamako mai kyau ba. Ya kamata su gyara dabi’unsu. Allah Ya shiryar da mu, amin.

Daga Aminatu B Ahmad Katsina.

 

Nasiha ga masoya

Gaisuwa a gare ku masoya wannan fili mai muhimmanci da kuma filin Sinadarin Rayuwa. Ina son isar da jinjina ga ogan wannan fili da dukkan masoya baki daya, da fatan Allah kara mana karfin gwiwa da basira tare da tunatarwa, fadakarwa, shiryarwa tare da nasiha; wadda za ta amfanar da mu baki daya. FDk, a fadakar da masoya yadda za su rike junansu da gaskiya da amana da zuciya daya kuma don Allah don samun dawwamammar kaunar juna ta har abada, Allah kara mana son manzon Allah (s.a.w) tare da koyi da shi a harkokinmu na yau da kullum, amin.

Daga Hussain Danjari Umar Kadarko-Katsina, 08038810162

 

Fatan Alheri Daga Fadar FDk

1-Aliyu Hydar Tudun Wada Kaduna.

2-Ummi Salma Sulaiman.

3-S. Umar Malumfashi, 07019928756.

4-Hussaini Adamu Makole-Kano.

5-Baban Abbas Kano, 08033996529.

6-Magaji Safaya Masukwari.

7-Lawal Musa Abuja, 07086468142.

8-Aliyu Mukhtari Zangon Daura.

9-Umar Kano Sarkin Yakin FDk, 07035438533.

10-Usman Ladan Silame, 08093075822.

11-Musa G. G. C. Kurna-Kano.

12-Rabi’u Ahmad Bebeji Kano.

13-Sanusi Musa Securety Gusau-Zamfara.

14-Umar Faruk DKD, 07067917833.

15-Abdul Funtuwa, 08182357976.

16- Mustapha Anka, 08037558407